Mazauna gaɓar Kogin Benuwe sun soma ƙaurace wa gidajensu

Manoma sun duƙufa wajen girbe amfanin gonakinsu da suka nuna.

Mazauna gaɓar Kogin Benuwe sun soma ƙaurace wa gidajensu

Mazauna yankin da ke gaɓar Kogin Benuwe a Jihar Taraba sun fara ƙaurace wa gidajensu tare da kwashe amfanin gonakinsu.

Wani mazaunin garin Ibbi da ke gaɓar Kogin Benuwe, Jalo Ibbi, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa wasu waɗanda gidajensu ke gab da gaɓar kogin a garin sun fara kwashe kayayyakinsu daga gidajensu domin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa.

Ya ce Kogin Benuwe a garin na Ibbi ya soma cika da ruwa a sanadiyar sako ruwa da aka yi daga Madatsar Ruwa ta Lagdo da ke ƙasar Kamaru.

Jalo Ibbi, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa tun ranar Alhamis aka ga ruwa ya soma shigowa Kogin Binuwai yana mamaye wasu gonaki musamman gonakin shinkafa.

Ya ce ganin haka wasu masu gidaje da ke gaɓar kogin suka soma kwashe kayayyakinsu suna kaiwa wasu gidajen ’yan uwansu da ke nesa da bakin Kogin.

A garuruwan Amar da Kambari waɗanda dukkan su da ke gaɓar kogin, mazauna sun fara kwashe kayayyakinsu daga gidajensu a yayin da manoma kuma suka duƙufa wajen girbe amfanin gonakinsu da suka nuna.

A garin Zip da Mayoreneyo da ke Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido, mazauna garuruwan sun shaida wa wakilin Aminiya cewa tuni ruwa ya shigo har ma ya mamaye gonaki.

Alhaji Gambo Zip, ya bayyana cewa masu gidaje da ke daf da bakin kogi sun fara ƙaurace wa gidajen suna komawa wasu wuraren da ke nesa da bakin kogi da ake kira Jigawan Zip.

Ya ce a duk lokacin da aka samu ambaliyar ruwa, mazauna garin can suke komawa har sai ruwan ya janye.

Alhaji Jidda Mayoreneyo, shi ma ya bayyana cewa ruwa ya cika kogi a garin na Mayoreneyo wanda babbar alama ce da ke nuna cewa an sako ruwa daga Madatsar Ruwa ta Lagdo.

Ya ce an samu aukuwar ambaliyar ruwa a yankin a kwanakin baya, inda manoma suka yi asarar amfanin gonakinsu, “yanzu kuma ga wata alama ta sabuwar ambaliya da ka iya faruwa a yankin.”

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato