Mazauna karkara na neman daukin ruwan sha a Gombe

Mazauna yankunan sun koka game da tsananin zafi da matsalar karancin ruwan sha.

Mazauna karkara na neman daukin ruwan sha a Gombe

Al’ummar wasu yankunan karkara da ke Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe, sun roki gwamnatin jihar da ta kai musu daukin ruwan sha.

Mazauna yankunan 11 da yawansu ya kai mutum 2,000 sun koka game da tsananin zafi da matsalar karancin ruwan sha.

Da yake zantawa da Aminiya a madadin al’ummar yankunan, Malam Idris Abubakar, ya ce matsalar karancin ruwan sha a cikin al’ummar babban kalubale ne.

“Yanzu lokaci ne na azumin Ramadan, halin da muke ciki na tsananin zafi ya yi munin da har ba ma iya samun ruwan sha na buda baki mai tsafta.”

Ya yi kira da gwamnati ta samar musu da ruwan sha, ko kuma gina musu rijiyoyin burtsatse.

Abubakar, ya kara da cewa suna neman dauki albarkacin wannan wata na Ramadan gwamnati ko shugabanin al’umma su dube su da idon rahama, su kai musu dauki.

Al’ummar yankunan da abin ya shafa sun hada da; Akko, wuro shafi, Garin Baraya, Malam Jamo, Gamadadi, Konkeje da Tongo.

Sauran al’ummomin da matsalar ta shafa sune Lawanti, Jalingo, Dunomari, Pagege da Marori wanda nisan su bai wuce kilomita 10 daga babban birnin, Jihar Gombe ba.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta