Mazauna kauyen Dutsen Zuma sun nemi agajin gwamnati

An bayyana kauyen Dutsen Zuma, wanda a baya yake karkashin Hukumar Birnin Tarayya Abuja kafin a mayar da shi karkashin karamar Hukumar Suleja da ke Jihar Neja a yanzu, da cewa shi ne kauye mafi koma baya a wannan rukuni ta fuskar kayan more rayuwa, don haka mazauna kauyen suke neman hukuma da ta kawo […]

Mazauna kauyen Dutsen Zuma sun nemi agajin gwamnati

An bayyana kauyen Dutsen Zuma, wanda a baya yake karkashin Hukumar Birnin Tarayya Abuja kafin a mayar da shi karkashin karamar Hukumar Suleja da ke Jihar Neja a yanzu, da cewa shi ne kauye mafi koma baya a wannan rukuni ta fuskar kayan more rayuwa, don haka mazauna kauyen suke neman hukuma da ta kawo masu dauki.

Aminiya ta gano cewa, wannan kauye na daga bangaren dama idan an taho daga Kaduna, inda titi ya raba dutsen da wannan kauyen, sannan unguwar na daga hannun hagu idan an bar garin Abuja zuwa Kaduna, idan an bi ta Zuba, daidai inda sojoji suke duba ababen hawa.

Mai Unuguwar Dutsen Zuma, Malam Muhammadu Dallatu ya shaida wa Aminiya cewa, “Kakannin-kakanninmu da iyaye duk a nan suka rayu kuma a yanzu muna karkashin Dagacin Gwazunu, muna bin Kansilan Madalla, karkashin Masarautar Suleja, inda tsohon Gwamnan Jihar Neja kuma Sarkin Suleja da ke kan karagar mulki Alhaji Awwal Ibrahim yake sarauta a karkashin karamar Hukumar Suleja da ke cikin Jihar Neja.”

Ya ce albakacin sun yi maraba da baki a kauyen sai Hausawa da sauransu suka ce su fara aikin-gayya kafin gwamnati ta kawo musu tallafi. Haka ya sa suka sami fili aka samo itatuwa da katakai suka kafa aji wanda aka rufe da katako, inda aka fara karatun firamare a ciki, inda daga baya suka gina ajujuwa biyu, sannan hukumar ta sama musu ajujuwa hudu, ta zama cikakkar firamare mai ajujuwa shida.

Bincike ya nuna cewa suna dangane da rowan sha, rijiyar burtsatse guda daya tak da aka gina tun 2012 mai aiki da hasken-rana. Famfunan tuka-tuka guda biyu da ke kauyen sun dade da lalacewa kuma ba su aiki, ba su da rijiya rkwakware. dakin shan maganinsu yana da gado daya ne kacal. Ba su da karamar sakandare ko akwatin zabe ko ofishin ’yan sanda, ba su da wutar lantarki da sauransu.

Mai Unguwar ya ce, “Mu kabilar Koro ne, mu mutane ne masu son zaman lafiya da saukar da baki, don haka muke rokon a tallafa mana don ba mu taba kawo cikas ga hukuma da doka ba. Rashin makarantar sakandare ya sa wasu yaran ba su ci gaba da karatu, wasu kuma sai sun tafi garin Madalla ko Zuba da sauran wurare don yin karatun jeka-ka-dawo. Ran da iyaye ba su ba yara kudin mota ba ba za su iya zuwa makaranta ba, wasu kuma in sun tafi a kan keke mota tana ture su sakamakon tsallake babban titin Abuja zuwa Kaduna.”

Ya kara da cewa mutanen kauyen sun kai mutane dubu goma, da gidaje dubu biyu da suka hada da Koro, Hausawa, Kalaba, Igbo, Yarabawa da sauransu.