Mazauna Saudiyya 60,000 ne kadai za su yi aikin Hajjin bana

Tun bayan bullar cutar COVID-19 ake samun ragin adadin mutanen da za su aikin hajji.

Mazauna Saudiyya 60,000 ne kadai za su yi aikin Hajjin bana

Masarautar Kasar Saudiyya ta sanar da cewar iya mutum 60,000 ’yan asalin kasar da wanda suke zaune a cikin kasar ne kadai za su yi aikin Hajjin bana.

Shafin Haramai Sharifain da ya sanar da hakan ya ce wannan na zuwa ne a matsayin wani mataki na ci gaba da yaki da kuma dakile cutar COVID-19 a fadin duniya.

  1. An rufe Kwalejin Nuhu Bamalli da ke Zariya
  2. Ganduje ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyin fadan daba a Kano

Mutum 60,000 da ke zaune a kasar, ciki har da wadanda ba ’yan asalin kasar ba na da damar yin aikin hajjin a bana, kamar yadda sanarwa ta gabatar a ranar Asabar.

Kazalika, Hukumar Lafiyar Kasar ta bayyana cewar tilas ne, ga wanda zai yi aikin hajjin a bana, ya kasance ya karbi akalla rigakafin allurar COVID-19 kashin farko, tare da killace kansa na tsawon mako biyu.

Tun a cikin watan azumi, kasar ta sanar da adadin mutum 60,000 a matsayin wanda za su aikin hajjin bana, amma ba ta ba da cikakken bayanin wanda zai halarta ba sai a yanzu.

A shekarar da ta gabata ma mutum 10,000 ne kacal suka gudanar da aikin Hajjin sakamakon bullar cutar COVID-19.

Sai dai a wannan shekarar, an samu karin adadin mahajjata da za su yi aikin hajjin fiye da na bara.