Mazauna Suleja za su fara biyan harajin Naira 200 ta waya

Shirye-shirye sun kankama a tsakanin karamar Hukumar Suleja da kamfanonin sadarwa domin karbar harajin tsabtace muhalli daga wajen magidanta da ke yankin ta hanyar zabtare Naira 200 duk wata daga wayoyinsu. Shugaban karamar Hukumar Suleja, Malam Ahmad Dikko kassim ne ya bayyana haka a wurin wata zama ta keke-da-keke a tsakanin al’ummar yankin da gwamnatinsa […]

Mazauna Suleja za su fara biyan harajin Naira 200 ta waya
Mazauna Suleja za su fara biyan harajin Naira 200 ta waya

Shirye-shirye sun kankama a tsakanin karamar Hukumar Suleja da kamfanonin sadarwa domin karbar harajin tsabtace muhalli daga wajen magidanta da ke yankin ta hanyar zabtare Naira 200 duk wata daga wayoyinsu.
Shugaban karamar Hukumar Suleja, Malam Ahmad Dikko kassim ne ya bayyana haka a wurin wata zama ta keke-da-keke a tsakanin al’ummar yankin da gwamnatinsa a bikin cikarta kwana dari, wanda ya gudana a harabar karamar hukumar.
A yayin taron wanda ya samu halartar hakimai da dagatai da ’yan siyasa da shugabannin al’ummar yankin, shugaban ya ce Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya ayyana kawo karshen asusun hadin gwiwa a tsakanin gwamnatin jihar da kananan hukumomi, inda ya ce daga karshen wannan wata kudin kowace karamar hukuma daga Abuja zai je gare ta kai-tsaye.
Shugaban ya ce “Sai dai abin bakin ciki kananan hukumomi takwas ne kadai daga cikin 25 na jihar ne za su amfana da hakan saboda ma’aikatansu kadan ne kudinsu ne ake ragewa a kara wa masu ma’aikata da yawa, kuma karamar hukumarsa tana cikin wadanda za su yi ta kansu don nemo hanyar cike gibin da hakan zai haifar.
Malam Ahmad Dikko, ya bayyana bakin cikinsa a kan yadda aka rika daukar ma’aikata a karamar hukumar ba tare da bukatar haka ba a baya, sai dai don samawa abokan tafiya aiki alhali ba abin da za su yi sai karbar albashi.
Ya ce karamar hukumar ta tantance ma’aikata har sau uku ba tare da ta gano na bogi ba, saboda haka zabin da ya rage mata shi ne korar ma’aikatan da ba su da aikin yi, ko rage albashin ma’aikatan ko kuma kirkiro sababbin hanyyoyin tara kudin shiga kamar yadda Gwamnan jihar ya ba su shawara a yayin zaman da su ka yi da shi na ayyana kawo karshen asusun hadin gwiwar. “Ba zan iya korar ma’aikata ba a wannan hali da ake ciki yanzu, kuma ba zan rage albashi ba, saboda haka zan kirkiro da sababbin hanyoyin kudin samun shiga. Daga ciki akwai tsarin karbar haraji daga wajen magidanta ta waya na Naira dari bibbiyu duk wata, idan magidanta sun kai biyar a gida guda kowannensu zai ba da lambar wayarsa da za a rika zabtare Naira dari biyu duk wata, wannan kudi zai taimaka wajen sayen karin motocin kwashe shara, saboda na tabbata kowane magidanci yana samar da shara a gidansa za a rika bi ana karba.”
“Haka masu shago da sauran sana’o’i za su rika biyan haraji kamar yadda aka saba don inganta kananan asibitocinmu da sauran ayyuka. Kuma karamar hukuma ta kulla yarjejeniya da sananannen likitan nan da ke aiki a Amurka Dokta Ladan wanda dan asalin yankin ne inda ta ba shi fili rabin hekta da zai gina masana’antar sarrafa shara zuwa wani abu mai amfani don samar da aikin yi ga jama’ar yankin da kuma kudin shi ga karamar hukuma. Ganin haka ya kawo mana wani abokinsa Bature da shi ma muka ba shi rabin hekta na fili da zai gina wata masana’anta,” inji shi.