Mazauna unguwa sun yi zanga-zanga kan sace mutane 6 a Kaduna
’Yan sanda sun bayyana cewa suna ci gaba da ƙoƙari domin ganin an kuɓutar da waɗanda aka sace.
Mazauna unguwar Danhono II da ke Millennium City a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin biyo bayan sace wasu ’yan unguwar su shida da ake zargin ’yan bindiga ne suka yi.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare wayewar gari Litinin, lokacin da wasu ’yan bindiga suka mamaye yankin suka yi awon gaba da mutanen daga gidajensu.
- Matashi ya mutu yayin ciro tukunyar gas a cikin rijiya
- NUJ ta buƙaci NEDC ta yi wa ’yan jarida inshora
Aminiya ta ruwaito cewa aukuwar hakan ta jefa al’umma cikin fargaba, lamarin da ya sa matasa, mata da sauran mazauna yankin suka fito kan tituna suka yi tattaki har zuwa ofishin ’yan sanda na yankin domin gabatar da ƙorafe-ƙorafensu kan tabarbarewar tsaro.
Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wasu matasa suna bayyana damuwarsu kan sake dawowar sace-sace a yankin.
Binciken Aminiya ya kuma gano cewa kusan makonni huɗu da suka gabata ne aka sace wani tsohon ɗan jarida, Malam Umar a gidansa da ke unguwar, kuma har yanzu yana hannun masu garkuwa da mutane duk da cewa an biya kuɗin fansa.
Wani jagoran matasa a yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa mazauna unguwar sun ji ƙarar harbe-harbe da misalin ƙarfe 12 na dare kafin daga bisani aka tabbatar da sace mutane shida.
“Zanga-zangar na zuwa ne sakamakon yawaitar sace-sace a yankin, musamman na bayanan wanda aka sace mutanen shida. Abin takaici ne yadda mazauna ke rayuwa cikin fargaba, har ma suna tsoron kwana a gidajensu,” in ji shi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce rundunar ta karɓi masu zanga-zangar tare da tura jami’ai zuwa yankin.
“Mun karɓi koken masu zanga-zangar, kuma tuni aka tura jami’ai zuwa yankin. Haka kuma ana ci gaba da ƙoƙari domin ganin an kuɓutar da waɗanda aka sace,” in ji DSP Mansir Hassan.