Mazaunin Benin ya yaba da ’yar majalisa mai wakiltar Yola ta Kudu
An yaba wa ’yar Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Yola ta Kudu Hajiya A’ishatu Ahmed Tahir Binani, bisa ayyukan taimakawa da take yi na ci gaban al’ummar Jihar Adamawa; kamar yadda dan asalin jihar kuma dan kasuwa mazaunin garin Benin, Alhaji Salihu Adamu Gangwaso ya tabbatar. Gangwaso ya yi yabon ne a yayin wata zantawar […]
An yaba wa ’yar Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Yola ta Kudu Hajiya A’ishatu Ahmed Tahir Binani, bisa ayyukan taimakawa da take yi na ci gaban al’ummar Jihar Adamawa; kamar yadda dan asalin jihar kuma dan kasuwa mazaunin garin Benin, Alhaji Salihu Adamu Gangwaso ya tabbatar.
Gangwaso ya yi yabon ne a yayin wata zantawar da ya yi da Aminiya a makon da ya gabata a garin Benin Jihar Edo, inda ya yaba da irin kwazon ’yar majalisar. Ya ce: “Ta taimaka wa al’ummar jihar domin taimakon nata bai takaita ga mazabarta kadai ba. Ta taimaka wa bangaren kiwon lafiya da fannin makarantar yara da kuma bangaren tsaftataccen ruwan sha. Ta sa an gina rijiyoyin burtsatse a yankuna da dama cikin mazabarta da sauran yankuna a cikin jihar.”
A karshe, dan kasuwar sai ya jinjina wa Gwamnan Jihar Adamawa, Adamiral Murtala Nyako tare da mai martaba Lamidon Adamawa, Dokta Muhammadu Barkindo Aliyyu Mustafa saboda abin da ya ce, jajircewarsu a kan fadin gaskiya na nema wa ’yan Najeiya, musamman ’yan Arewa hakki na zaman lafiya.