Mbappe ya sake kafa sabon tarihi a Gasar Kofin Duniya
A yanzu Faransa za ta kara da Paraguay a zagaye na 16.
Kyaftin ɗin tawagar Faransa, Kylian Mbappe, ya sake kafa sabon tarihi a Gasar Kofin Duniya bayan ya zura ƙwallaye biyu a wasan da ƙasarsa ta doke Sweden da ci 3-0, lamarin da ya ba su damar tsallaka wa zagayen ’yan 16.
Mbappe ya zama ɗan wasa na farko da ya ci ƙwallaye 10 a wasannin siri ɗaya ƙwale na Gasar Kofin Duniya.
- Amurka za ta ɗauki wasu matakai idan tattaunawa da Iran ta ci tura — JD Vance
- Lampard zai jagoranci Coventry a kakar wasanta ta farko a Firimiya cikin shekaru 25
Haka kuma ya kai jimillar ƙwallaye 18 a tarihin gasar, inda ya rage ƙwallo guda ɗaya ya yi kunnen doki da Lionel Messi mai 19.
Bradley Barcola ne ya ƙara ƙwallo ta uku, inda Faransa ta tabbatar da matsayinta na tsallaka wa zagaye na gaba.
Da wannan nasara da Faransa ta samu, mai horar da tawagar, Didier Deschamps, shi ma ya kai wani sabon matsayi a tarihin gasar, yayin da tawagarsa ke ci gaba da nuna ƙwarewa a fafatawar bana.
A yanzu Faransa za ta kara da Paraguay a zagaye na 16.