Mbappe zai yi jinyar sati 3 sakamakon rauni

Ɗan wasan ba zai buga wasan hamayyar Real Madrid da Atletico Madrid

Mbappe zai yi jinyar sati 3 sakamakon rauni

Ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Kylian Mbappe zai yi jinyar sati uku, biyo bayan raunin da ji a ranar Talata.

Likitocin ƙungiyar sun tabbatar da cewar ɗan wasan ya samu rauni ne a wasan da Real Madrid ta doke Alaves da ci 3 da 2.

Tuni Real Madrid ta fitar da sanarwa game da raunin da ɗan wasan ya ji.

Mbappe ba zai buga wasan da Real Madrid za ta yi da abokiyar hamayyarta, Atletico Madrid a ƙarshen mako mai zuwa.

Har wa yau, ɗan wasan ba zai buga wasanni bayan wasan hammayar na birnin Madrid da za a yi.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7