Mbursa Musa: Makahon da ke gyaran mota
Malam Mbursa Musa wani makaho ne da ke sana’ar gyaran mota a wani gareji da ke Unguwar Kanawa Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda lalurar makantar ba ta shafar aikinsa da wadansu daga cikin kalubalen da yake fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka? Mbursa Musa: […]

Malam Mbursa Musa wani makaho ne da ke sana’ar gyaran mota a wani gareji da ke Unguwar Kanawa Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda lalurar makantar ba ta shafar aikinsa da wadansu daga cikin kalubalen da yake fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?
Mbursa Musa: Assalamu alaikum, sunana Mbursa Musa, an haife ni ne a ranar 26 ga watan Oktoban shekarar 1964, a garin Garkida na karamar Hukumar Gombi da ke Jihar Adamawa. Na yi makarantar firamare, inda na kammala a shekarar 1976. Ban ci gaba ba saboda wasu dalilai. Daga nan a shekarar 1978 sai na taho Kaduna.
Aminiya: Wace sana’a ka fara da ita?
Mbursa Musa: Na fara ne da sana’ar gyaran mota wacce ita nake yi har yanzu. Na koye ta ne a wajen wani mai gidanmu da ake kira JbC. Daga nan sai a shekarar 1981 ya yaye ni, wato abin da wasu ke kira Freedom. Bayan haka, sai na koma wani gareji kusa da Hamdala Otel Kaduna. Muka ci gaba da koyon gyaran wasu samfarin motoci kamar su: Honda da Toyota da kuma bolbo da sauransu. Domin a wurin mai gidana na farko na koyi gyaran Peugeot ne kawai. Da na sanya hankalina a wurin sosai, sai na koyi duka gyaran wadannan motocin. Daga bisani, ni da wani abokina mai suna Bello mun dawo nan Unguwar Kanawa, inda muka kafa wannan garejin da muke wannan tattaunawar, a shekarar 1993. Garejin hadin gwiwa ne, wannan ya sa kowane wata muke raba duk abin da muka samu a tsakaninmu bayan mun biya yaran da muke aiki tare da su.
Aminiya: Me ya ja hankalinka zuwa sana’ar gyaran mota?
Mbursa Musa: Tun lokacin da nake makarantar firamare idan muka fita wasa wato lokacin break, sai in tafi wurin da wadansu Turawan Mishan ke gyaran mota in zauna ina kallonsu. Har ta kai ga cewa mun saba sosai ba wurin da bana shiga a cikin garejin. Sai ya zama kamar na fara koyon aikin tun a wurin. Wannan ya sa koda zuwa na Kaduna da aka tambaye ni wace sana’a na fi so sai na ce gyaran motoci.
Aminiya: Yaushe ne wannan lalurar rashin gani ta same ka?
Mbursa Musa: Lalurar makantar ta same ni ne a shekarar 1993. Daga nan na je asibitoci daban-daban domin neman magani, amma ba tare da samun nasara ba. An yi mini aiki a idanuna har sau uku, ciki har da wanda aka yi mini a babban asibitin ido da ke nan Kaduna wato National Eye Centre, amma labarin bai sauya ba. Likitoci sun shaida mini cewa makantar ta faru ne sanadiyyar ciwon Glaucoma wanda wasu ke kira hawan jinin ido. A lokacin sun ce duk wata kulawa da za su ba ni za ta tsayar da ciwon ne kawai, amma ba wai zan warke ba ne gaba daya. Haka dai ma ganina ya yi ta raguwa har ya zama babu.
Aminiya: Bayan faruwar makantar, ta yaya ka ci gaba da sana’arka?
Mbursa Musa: Da taimakon wadanda muke tare har yanzu ina gudanar da aikina, ina kuma bayar da shawarwari. Har ila yau, ina zama cikin mota sai wani ya tuka bayan na saurari kukan motar, sai na bai wa yarana umarnin a kwance wancan, a daure wancan da dai sauran abubuwan da suka sauwaka. Idan kuma aikin da aka bukata na ido ne, ina da mayan yara da kanana sai na ce wane ga aiki ka yi. A wasu lukutan kuma ina zama da kaina na hada inji, idan akwai mai ido kusa da ni da za mu yi aikin tare. Muna hada inji tsaf. A gama su dauka a saka kuma ya tashi kunnawa daya.
Aminiya: Wane martani kake samu daga wadanda ka yi wa aiki?
Mbursa Musa: Har yanzu wadanda nake wa aiki suna jin dadin aikina saboda sukan nuna gamsuwarsu a lokuta da dama. Akwai wasu da suke cewa sun fi son gyarana fiye da na masu ido.
Aminiya: Ko akwai wani kalubale da kake fuskanta?
Mbursa Musa: Ah, kalubalen da nake fuskanta shi ne yawancin motocin zamani da na’urar kwamfuta ake gyara su. To ni kuma wadannan abubuwan yanzu, sai dai wani ne ya yi, amma ni ba zan iya ba. Saboda ba zan gane abin da kwamfutar ta fadi ba. Kuma ma ba mu da ita a garejinmu, sai mun kai wani wuri.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu albarkacin wannan sana’ar?
Mbursa Musa: A gaskiya mun gode wa Allah, albarkacin wannan sana’ar ina da da da ya yi karatu har zuwa matakin jami’a da sauran da suke kwalojojin horar da malamai da makarantar sakandare da sauransu. Hakazalika, idan muka dawo bangaren bai wa wadansu horo kan wannan sana’ar. Na bai wa yara da dama horo kuma a yanzu haka bayan wanda muka kafa kamfanin nan tare da shi, muna da wadanda suke karkashinmu akalla mutum 70.
Aminiya: Kana da wani buri?
Mbursa Musa: A gaskiya idan zan samu taimako yanzu musamman idan zan samu na’urar kwamfuta zan ji dadin aikin sosai. Daga nan sai na samu wanda musamman zai dinga kula da ita, inda za mu rika aiki tare da shi.
Aminiya: Ya batun iyali fa?
Mbursa Musa: Ina da mata daya da ’ya’ya bakwai.