MDD ta fara bincike kan zargin tsangwamar Kiristoci a Najeriya

A baya-bayan nan, wasu jami’an Amurka sun yi zargin cewa Kiristoci na fuskantar tsangwama a Najeriya.

MDD ta fara bincike kan zargin tsangwamar Kiristoci a Najeriya

Nazila Ghanea

Wata ƙwararriyar jami’a ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) kan ’yancin addini da aƙida, Nazila Ghanea, ta fara wata ziyara ta makwanni biyu a Najeriya domin tantance halin da ake ciki dangane da ’yancin addini a ƙasar.

Ziyarar ta zo ne bayan muhawara da zarge-zargen da suka ɗauki hankalin ƙasashen duniya a bara kan batun cin zarafin Kiristoci a Najeriya.

Ghanea za ta ziyarci birnin Abuja da Kano da kuma Jos a Jihar Filato, domin ganawa da hukumomi da masu ruwa da tsaki tare da nazarin kalubalen da ke tattare da ’yancin addini da akida.

Sanarwar MDD ta ce manufar ziyarar ita ce gano matsalolin da ake fuskanta da kuma sabbin ƙalubalen da ka iya hana mutane gudanar da addininsu cikin ’yanci.

Najeriya, mai yawan jama’a da suka haura miliyan 230, na da mabiya addinan Musulunci da Kiristanci da ke rayuwa tare a yankuna da dama cikin lumana.

Sai dai ƙasar ta sha fama da rikice-rikicen addini da na ƙabilanci a lokuta daban-daban, musamman a wasu sassan arewa da yankin Filato.

A baya-bayan nan, wasu jami’an Amurka sun yi zargin cewa Kiristoci na fuskantar tsangwama a Najeriya, zargin da gwamnatin Najeriya ta musanta tare da cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta ba su da alaƙa kai tsaye da addini.

Masana da masu bincike sun bayyana cewa rikice-rikicen da ake samu tsakanin makiyaya da manoma, waɗanda galibi ke haɗa Musulmai da Kiristoci, sun fi nasaba da rikicin ƙasa da iyaka, ƙarancin albarkatu da sauyin yanayi, ba wai addini kaɗai ba.

Ana dai sa ran Ghanea za ta fitar da rahoto da shawarwari bayan kammala ziyararta a Najeriya.