MDD ta gaza ɗaukar mataki kan yaƙin Gaza —Erdogan
Erdogan ya zargi Isra’ila da mayar da yankin Falasɗinu a matsayin maƙabartar binne mata da ƙananan yara
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya caccaki Majalisar Ɗinkin Duniya saboda rashin ɗaukar mataki kan yaƙin Gaza, yana mai zargin Isra’ila da mayar da yankin Falasɗinu a matsayin maƙabartar binne mata da ƙananan yara.
Kazalika shugaba Erdogan da ke magana a zauren taron Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin New York na Amurka, ya nuna goyon bayansa ga Lebanon wadda Isra’ila ke ci gaba da yi mata luguden wuta da nufin kakkaɓe mayaƙan Hezbollah, inda kuma ya soki gwamnatin Benjamin Netanyahu da ƙoƙarin jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin yaƙi.
“Ba ƙananan yara kaɗai ke mutuwa ba a Gaza, hatta tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya shi ma yana mutuwa a yankin,” Inji Erdogan
Erdogan ya kuma ɗiga ayar tambaya kan sahihancin ayyukan ƙungiyoyin ƙare hakkin bil’adama na duniya, yana mai cewa, shin ba mutane ba ne ke rayuwa a Gaza da kuma Gabar Yamma da Kogin Jordan?
- Duk da man Dangote, wahalar fetur ta dawo a Abuja
- DAGA LARABA: Dalilin Da ’Yan Najeriya Ke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?
Har ila yau, shugaban na Turkiyya ya caccaki Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya kan gazawarsa wajen bayar da umarnin dakatar da yaƙin Gaza, inda ya ce mambobin kwamitin sun zura ido suna kallon yadda ake aiwatar da kisan kiyashi a yankin.
Erdogan ya kuma kwatanta Netanyahu da jagoran sojojin Nazi, Adolf Hitler, inda ya buƙaci ƙasashen duniya da su yi duk mai yiwuwa domin dakatar da shi daga kashe-kashen da yake yi a cewarsa.
Hukumomin Gaza sun ce, akalla mutane dubu 4i da 467 ne Isra’ila ta kashe a jerin hare-haren da take ƙaddamarwa a yankin tun bayan da Hamas ta kai wani hari a ranar 7 ga watan Oktoban bara cikin Isra’ila wanda ya halaka mutane dubu 1 da 215.
Ba za mu bari Isra’ila ta kori Falasɗinawa ba – Sarkin Jordan
Sarkin Jordan Abdullah na biyu ya ce akwai yiwuwar ƙasarsa ta zama tudun-mun-tsira ga Falasɗinawa, yana mai gargaɗin cewa, raba su da muhallansu da Isra’ila ke yi ka iya zama laifukan yaƙi.
Shi ma Sarki Abdullah na magana ne a gaban shugabannin ƙasashen duniya a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, yayin da ya jaddada cewa, ba za su taɓa bari a sauya wa Falasɗinawa matsugununsu ba zuwa Jordan kamar yadda wasu masu tsattsauran ra’ayi ke buƙata.
Sarkin ya ce, Jordan ba za ta amince a raba Falasɗinawa da muhallansu ba saboda haka tamkar aikata laifukan yaƙi ne a cewarsa.
Jordan dai ta haɗa iyaka da Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila, sannan tana da ɗimbin Falasɗinawa da ke zaune a cikinta.
Sarkin ya kuma roki shugabannin ƙasashen duniya da su agaza wa mutanen Falasɗinu da ke cikin matsananciyar buƙatar abinci da ruwan sha da magunguna da sauran kayayyakin buƙatar ɗan Adam.
“Duniyarmu ta gaza ta fannin siyasa, amma bai kamata tausayinmu ya gaza isa ga mutanen Gaza ba” Inji Sarki Abdullah.
Shugaba Biden ya yi gargadi kan yakin Gabas ta Tsakiya
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi gargaɗin tsanantar yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai rokon shugabannin ƙasashen duniya da su samar da hanyar diflomasiyya wajen warware rikicin Lebanon da Gaza.
“Tsanantar yaƙi, ba ita ba ce burin kowa,” Inji Biden.
Jawabansa a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya na zuwa ne a yayin da Isra’ila ke ci gaba da ragargazar Lebanon da makamai da nufin kakkaɓe mayaƙan Hezbollah, yayin da aka samu asarar rayukan mutane sama da 500.
Zubar da jinin da ake yi a Lebanon na zuwa ne bayan watannin da Amurka ta kwashe tana ƙoƙarin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita musayar wuta tsakanin Isra’ila da Hamas a yaƙin Gaza, amma lamarin ya ci tura.
Shugaba Biden ya ce, har yanzu yana ci gaba da ƙoƙarin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita wutar tsakanin ɓangarorin biyu.