MDD Ta Nemi A Gaggauta Muradun Ci Gaba Mai Ɗorewa Don Cimma Burin 2030

MDD ta bayyana sha’awa kan sabbin hanyoyin fasaha da matasa ke gabatarwa.

MDD Ta Nemi A Gaggauta Muradun Ci Gaba Mai Ɗorewa Don Cimma Burin 2030

Ko’odinetan MDD a Nijeriya, Mohammed Malick Fall

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gaggauta samar da ci gaba mai ɗorewa a Nijeriya domin cimma burinta nan da zuwa 2030.

Ko’odinetan MDD a Nijeriya, Mohammed Malick Fall ne ya bayyana hakan bayan ya kammala ziyarar aiki ta mako guda a jihohin Legas, Enugu, da Anambra.

Sanarwar da jami’in yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya, Oluseyi Soremekun, ya fitar a ranar Alhamis, ta ce ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da aka fitar da rahoton muradun ci gaba mai dorewa na 2024, wanda ya bayyana cewa kashi 17 cikin 100 ne kawai na manufofin SDG ake da su a halin yanzu kan hanya.

A yayin ziyarar tasa, Fall ya tattauna da gwamnoni, kwamishinoni, shugabannin kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya, da kungiyoyin mata da matasa.

Ya jaddada bukatar a hanzarta aiwatar da bukatar cimma buri don inganta jin dadin mutane da duniya baki daya.

A Enugu, Gwamna Peter Mbah ya amince da daidaito tsakanin manufofin gwamnatinsa da umarnin Majalisar Dinkin Duniya da SDGs.

Fall ya yaba da sabbin hanyoyin da ya gani, musamman a makarantar Owo Smart.

“Ziyarar da na kai makarantar Owo Smart a Jihar Enugu, ta kasance bude ido da kuma tabbatar da cewa da shugabanci na gari, babu abin da zai gagara.

“Na ga yadda ake amfani da fasaha don tabbatar da ingantaccen ilimi, ta yadda za a dora dalibai kan turbar samun kyakkyawar makoma,” in ji shi.

A kuma Jihar Anambra, Fall ya gana da Gwamna Charles Soludo don tattauna batun rage radadin talauci, barazanar muhalli, da kare al’umma.

Ya kuma ziyarci kauyen Eziabor Oko, daya daga cikin sama da yankuna 1,000 da ake fama da zaizayar kasa a jihar, inda ya yi kira da a kawo dauki cikin gaggawa.

Ya ce, “Na ga wani wuri da ake fama da zaizayar kasa, wanda yake bukatar Gwamnatin Tarayya da gwamnatin jihar da dukkan masu hannu da shuni su kawo dauki domin ceton rayuka da rayuwa.

“Anambra na bukatar dukkan goyon bayan da za ta iya samu don dorewar magance kalubalen da ke tattare da zaizayar kasa a jihar.”

A Legas, Fall ya yi hulɗa da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu, ciki har da Tony Elumelu, Shugaban Kamfanin Heirs Holdings, UBA, da kungiyoyin Transcorp.

Ya jaddada muhimmiyar rawar da kamfanoni masu zaman kansu ke takawa wajen ciyar da tsarin ci gaba mai dorewa gaba tare da yaba gudunmawar Elumelu ga ci gaban matasa.

“Koyaushe abin farin ciki ne don yin hulɗa tare da ku da ƙungiyarku, koyaushe kuna yin la’akari da ƙuruciyar matasa a Nijeriya da Afirka da kuma rabe-raben jama’a. Matasa suna ba da damammaki masu yawa don ci gaban kasa,” in ji shi.

Fall ya kara bayyana makomar Taron Tasirin Al’umma na Afirka mai zuwa, ASIS2024, yana mai cewa zai taimaka wajen samar da fahimta kan yadda za a iya ceton dorewar ci gaba a Nijeriya da Afirka.

Babban jami’in na MDD ya bayyana sha’awa musamman kan sabbin hanyoyin samar da fasahar kere-kere da matasa ’yan kasuwa ke gabatarwa.

“Duba da cewa yawancin matasa sun rungumi fasaha da kirkire-kirkire, muna ganin za a dace wajen samun kyakkyawar makoma,” in ji Fall.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja