MDD za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da taimakon ’yan Najeriya — Amina Mohammed

Mataimakiyar Sakatare-Janar ta MƊD, Amina Mohammed, ta kammala ziyarar aiki a Najeriya

MDD za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da taimakon ’yan Najeriya — Amina Mohammed

Mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J. Mohammed ta jaddada cewa Majalisar Ɗinkin Duniya za ta karfafa haɗin gwiwarta da gwamnatin Najeriya tare da bayar da goyon baya ga ci-gaban al’ummar ƙasar.

Amina J. Mohammed ta kuma nemi goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya a yankin Yammacin Afirka tare da da daukar matakan yaƙar sauyin yanayi da dai sauransu.

A yayin ziyarar aikin kwana biyu da ta kammala a Najeriya, Mataimakiyar Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniyar ta yi tarurruka da dama, ciki har da Shugaba Bola Ahmed Tinubu; Ministan Kuɗi daTattalin Arziki, Wale Edun; Ministan Jinƙai, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda; manyan jami’an gwamnati; Shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen yammacin Afrika (ECOWAS), Dakta Omar Alieu Touray; da kuma tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya a karkashin jagorancin mai kula da ayyukan jin ƙai, Mohamed Malick Fall.

A cewatta, “Ƙasashe mambobi, ciki har da Najeriya, tare da goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran masu ruwa da tsaki, suna buƙatar ba da gudummawar don tabbatar da aminci da rayuwa mai kyau ga duniya da mutane a ko’ina.”

Ta kuma bayyana cewa yarjejeniyar da aka cimma wa a taron ƙoli da aka gudanar a watan Satumbar 2024 a birnin New York, ta kasance tabbatacciya ta hanyar dawo da muradun ci gaba mai ɗorewa (SDGs).

“Yarjejeniyar ba wata sabuwar ba ce daban da SDGs. Ɗaya cr shi ya sa babin farko ya kasance kan SDGs da kuma ba da kuɗaɗen ci gaba,” in ji ta.

Ta ci gaba da cewa, “ya shafi zaman lafiya da tsaro na duniya; kimiyya da fasahar zamani; matasa da na gaba; da kuma sauya tsarin mulkin duniya.”