MDD za ta dakatar da aikin agaji a Gaza saboda rashin mai

Nan da ’yan sa’o’i asibitocin da ke Zirin Gaza za su daina aiki saboda rashin man fetur, mastalar da ke neman hana ayyukan jinkan da Majalisar Dinkin Duniya ke gudanarwa a yankin Falasdinawan

MDD za ta dakatar da aikin agaji a Gaza saboda rashin mai

Ofishin Ayyukan Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Falasdinawa ya ce karancin man fetur na barazanar kawo karshen ayyukan agajin da yake gudanarwa a Zirin Gaza a daren Laraba.

Ofishin ya bayyana cewa rashin man na barazanar sa asibitoci su daina aiki, mako biyu bayan Isra’ila ta hana shiga ko fita daga irin Gaza.

A daren Talata jirage marasa matuka na Isra’ila suka kai hari a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke yankin Falasdinawa da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan, inda suka kashe Falasdinawa.

Kawo yanzu adaddin Falasdinawan da Isra’ila ta kashe daga ranar 7 ga wata ta fara luguden bama-bamai a Zirin Gaza ya haura 5,700, yawancinsu mata da kananan yara.

Al’ummomi a sassan duniya na ci gaba da zanga-zangar Allah-wadai da kisan gillan da Isra’ila ke yi a Gaza a mako uku da suka gabata.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres ya zargi Isra’ila da karya dokokin kasa da kasa a mamayar da take yi Zirin Gaza.