Me Anenih ke ci na baka na zuba?

Shugaban kwamitin amintattun ‘ya’yan jam’iyyar PDP, Cif Tony Anenih ya bukaci Shugaba Goodluck Jonathan da ya fito fili, a wata mai zuwa, ya fayyace matsayinsa game da takarar shugabancin kasa a 2015, domin kuwa lokaci ya yi da jam’iyyar za ta fara bayyana manufofinta ba tare da nuku-nuku ko kumbuya-kumbuya ba. Cif Anenih ya nuna […]

Me Anenih ke ci na baka na zuba?
Me Anenih ke ci na baka na zuba?

Shugaban kwamitin amintattun ‘ya’yan jam’iyyar PDP, Cif Tony Anenih ya bukaci Shugaba Goodluck Jonathan da ya fito fili, a wata mai zuwa, ya fayyace matsayinsa game da takarar shugabancin kasa a 2015, domin kuwa lokaci ya yi da jam’iyyar za ta fara bayyana manufofinta ba tare da nuku-nuku ko kumbuya-kumbuya ba. Cif Anenih ya nuna wa jiga-jiga ‘ya’yan jam’iyar PDP a Abuja cewa ba daidai ba ne a yi ta waskiya game da batun tsayawar Shugaba Jonathan takara, domin kuwa barin kashi a ciki bai maganin yunwa. Ya ce wajibi ne tun da sanyin safiya su fayyacewa mabiyansu inda suka dosa da kuma yadda tafiyar tasu za ta kasance. Batun sake takarar Shugaba Jonathan ya dade yana dagula al’amura a cikin jam’iyyar, wasu na taimaka masa don sake darewa, wasu kuma na yunkurin hana shi maimaitawa.
To yanzu dai dabara ta ragewa mai shiga rijiya, ga shugaban bokayen jam’iyyar nan ya share wa Jonathan fage, ‘ya’yan jam’iyyar PDP da ma sauran ‘yan siyasar kasar nan za su kasa kunnuwa su ji irin amsar da zai bayar, ganin yadda hakan zai canja al’amuran da ke wakana a siyasance a jam’iyyar, musamman ma saboda ya rigaya ya ce shi ba wannan ne ba a gabansa, zai ci gaba ne da mayar da hankalinsa ga harkar gudanar da mulkin kasa.
A ganin Shugaba Jonathan furta wata kalma game da haka na iya tayar da zaune tsaye a kasar, ayyukan gwamnatoci su tsaya cik, a yi ta kataniya da kata-kata a al’amuran gudanar da mulki. To idan kuwa haka ne Shugaba Jonathan ke nufi sai a ce sama da kasa ba za su hade ba idan ya ce zai tsaya takara ko ba zai tsaya ba. A yanzu ma da ayyukan gwamnatoci ke tafiyar sanda, ma’aikatan hukuma sun dulmuya cikin rashawa da ha’inci da cin hanci, ga yawan amaja a bakin aiki, kudurinsa na tsayawa takara ne ta hadasa haka?
Batun tsayawar Shugaba Jonathan ba abu ne da zai addabi kowa ba illa kawai ‘ya’yan jam’iyyarsa ta PDP wadanda ke ta hauragiya da tankiya game da rashin cancantarsa ta tsayawa takarar. Sauran ‘ya’yan jam’iyyun cewa suke yi ina ruwansu da wannan, domin a ganinsu lamarin bai shafe su ba, idan shugaba Jonathan ya yi sauri ko jinkirin fitowa ba abin da ya dada su da kasa, kuma zai kwashi kwashinsa a hannu idan har ya fiton.
Ba ma sai an fada ba kowa ya san cewa tun daga lokacin da aka rantsar da Goodluck Jonathan a matsayin shugaban kasa a 2011 sai ya kallafa ransa kan zarcewa domin kuwa ya lasa gardin mulki tun da farko, ya kuma ji dadi, ya kuma huda, ya ga jini. To abin tambaya game da haka ita ce da gaske ne  tabbacin da shugaba Jonathan zai bayar ta yin takara za ta iya tayar da zaune-tsaye a kasar nan kaman yadda yake zato? Amsar wannan tambayar ba mai wuya ce ba: ‘hakan ba zai yiwu ba’. Idan ma da cewa ya yi  ba shi ba takara a 2015 da hakan yafi nono fari, domin sun san yin haka ne kawai zai kawo lumann har ya samu daman mayar da hankalinsa kan tsarawa da gudanar da zaben da zai gamsar, sakamakonsa kuma ya kasance karbabbe ga daukacin al’ummomin kasar nan. Yin haka ne zai yayyafa ruwa ga kurar rikice-rikicen da suka mamaye jam’iyarsa sakamakon bakin burinsa na sake takara. To amma, ina! Al’amarin ba  haka ne ya kasance ba domin bisa ga dukkan alamu Shugaba Jonathan na son yin takara a zabe mai zuwa. To idan kuwa haka ne kada ya tsaya wata-wata, ya gaggauta fitar da maitarsa a fili  tun da sanyin safiya, ba wai ya tsaya  yana wasan buya da ‘yan jam’iyyar da suka kosa su ga bayansa ba.
Ya kamata  masu ra’ayin shugaba Jonathan su tsaya, su yi tunani, su kuma gwada shi da sauran ‘yan takaran da ke hankoron tsayawa takara a shekara 2015 daga cikin jam’iyyarsu don darje wanda zai fi cancanta  da dacewa wajen darewa karagar mulkin kasar. Idan dai har shugaba Jonathan na ganin cewa lokaci bai yi ba da zai furta ra’ayinsa game da tsayawa balle har ya fara fita yakin neman zabe, to ta yaya za a iya fassara yawan kadifiri da zakewar  da wasu kungiyoyi da ‘yan kabilarsa  ke yi don goyon bayansa?  To me Anenih ne ke ci na baka ya zuba? Jonathan zai fito zabe, talakawan Najeriya kuma za su taru, su nuna masa iyakarsa.