‘Me gaskiya ba zai tabe ba’
Assalamu alaikum Manyan Gobe, fatan alheri a gare ku, kuma. A yau na kawo muku wani labarin ‘Mai gaskiya ba zai tabe ba’. A duk inda kuka samu kanku, ku zama masu gaskiya don samun nasara a nan gaba. A sha karatu lafiya.An yi wani sarki wanda ya dade a kan mulki. Hakan ya sanya […]
Assalamu alaikum Manyan Gobe, fatan alheri a gare ku, kuma. A yau na kawo muku wani labarin ‘Mai gaskiya ba zai tabe ba’. A duk inda kuka samu kanku, ku zama masu gaskiya don samun nasara a nan gaba. A sha karatu lafiya.
An yi wani sarki wanda ya dade a kan mulki. Hakan ya sanya tsufa ta kama shi, inda ya fara tunanin ya nada wanda zai gaje shi daga cikin iyalansa ko mutanen gari. Rannan sai ya kira iyalansa da ‘yan gari, bayan sun taru a fadarsa sai ya ce: “Ina ganin ya kamata na bar kujerar mulki saboda tsufa.. Kuma ina son wanda zai gaje ni ya kasance daga iyalina ko mabiyana”. Iyalinsa suka yi mamaki game da abin da mahaifinsu ya fada.
Sarki ya ce zai ba kowa iri don ya shuka don gane wanda ya fi yin shuka mai yawa. Kuma ya yi alkawarin duk wanda irinsa ya girma shi zai gaje shi. Nan take kowa ya karbi iri sai ya wuce gida.
Akwai wani yaro ana kiransa Musa. Da ya je gida, sai ya ba mahaifiyarsa irin. Mahaifiyarsa ta ba shi tukunya inda zai shuka. Bayan sati daya, bai ga komai ba. Sati biyu har uku bai ga komai ba. Kuma ya gan na abokansa na ta girma har sun fara reshe.
Abokansa suka shiga yi masa dariya. Mahaifiyarsa dai ta ce masa ya ci gaba da ba shukar ruwa. Sai da aka shekara daya sai sarki ya ce kowa ya kawo shukarsa ya gani.
Musa ransa a bace har ya gaya wa mahaifiyarsa ba zai je taron da za a yi a wajen sarki ba don nasa irin bai girma ba. Mahaifiyarsa ta ba shi hakuri har ya yadda ya tafi da shukarsa zuwa fada.
Isarsa fada, sai ya ga na abokansa har sun girma sosai. Wasu daga abokansa na ta zolayarsa, wasu kuma su na jajenta masa. Can sai sarki ya fito. Da ganin sarki, sai Musa ya boye tukunyarsa a bayan abokansa. Sai sarki ya shiga neman wanda nasa irin bai girma ba. Nan sai ya ga Musa yana ta boyewa. Sai ya sa fadawa su kira shi. Da Musa ya ga fadawan, sai ya ce: “To, yau tasa ta kare.” don yana tsammanin kashe shi sarki zai yi.
Sai sarki ya shiga jawabi: “Yau na samu wanda zai gaji kujerata.” Sai ya nuna Musa. Kowa sai ya yi mamaki. Sai sarki ya ce ai irin da ya ba kowa nunanne ne kuma ba yadda zai tsiro. Musa ne kadai mai adalci kuma shi ne wanda ya cancanta a ba shi kujerar sarauta. Nan take aka nada wa Musa rawani ya zama sarki.
Da fatan Manyan Gobe za su rika fadin gaskiya don ita ce mafita kuma mai gaskiya ba zai taba tabewa ba.