Me Jonathan yake nema a 2015?

Watannin baya na ta~a tattauna batu makamancin wannan, sai dai da alama ko dai zancen da na nazarta bai kai ga gwamnatin Shugaba Jonathan ba ko kuma ya kai ga kunnen, amma ta yi kunnen-uwar-shegu da batun. Ba wani abu ya sa na fadi haka ba sai ganin cewa yanzun nan a jam’iyyar PDP ba […]

Me Jonathan yake nema a 2015?
Me Jonathan yake nema a 2015?

Watannin baya na ta~a tattauna batu makamancin wannan, sai dai da alama ko dai zancen da na nazarta bai kai ga gwamnatin Shugaba Jonathan ba ko kuma ya kai ga kunnen, amma ta yi kunnen-uwar-shegu da batun.
Ba wani abu ya sa na fadi haka ba sai ganin cewa yanzun nan a jam’iyyar PDP ba a batun komai sai takarar Jonthan shi kadai, bai da kini ko abokin tarayya. Kenan jam’iyyar PDP na nufin cewa abin da Shugaba Jonathan ya yi cikin shekarun nan abin tokabo ne, abin a yaba ne ko kuma abin da ya dace a ba shi damar kara zarcewa ne.
Ni dai ba dan siyasa ba ne, sai dai ina da damar a matsayina na dan kasa in ce uffan kan matakan da ake bi domin gudanar da rayuwata da ta sauran al’umma, wanda ke sa dole mutum ya tanka domin fadakar da hukuma ko don jan hankali domin a kula don gaba.
Tambayar da nake son yi a yau ita ce shin me kuma shugaba Jonathan ke bida a shekarar 2015 ko ma fiye? Shin da gaske ne ya yi abin a-zo-a-gani da za a sake ba shi irin wannan dama? Amsar wadannan tambayoyi da wasu irin su za su iya ba mu damar mu yanke hukunci kafin shekarar ta 2015.
Daga abin da gwamnatin ke fada ta kafafen watsa labarai muna iya cewa wannan gwamnatin ta Shugaba Goodluck Ebele Jonathan shin hangen Dala wai shiga birni ne? Shin abin da take fada game da ciyar da kasar nan gaba, hakan ne? Shin da gaske al’ummar kasar nan na cikin aljannar duniya ne daga tsare-tsaren gwamnatin a halin yanzu shi ya sa take son ta sake hayewa bisa karaga? Maimakon mu dubi komi da komi game da zaman dirshan din da gwamnatin ta yi na tsawon shekaru bari mu dauki bangare biyu kurum, na tsaron rayukan al’umma da kyautata jin dadin jama’ar kasar, mu ga ko jadawalin lissafin na bisa kan turba da alkalumma na gaskiya.
A cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya, babban kudirin da ke shimfide shi ne gwamnati ta tabbatar da tsaron lafiya da rayuka da kuma kyautata jin dadin al’ummar kasa. Wannan shi ne kowace gwamnati ya dace ta dasa a cikin kwakwalwarta domin a tabbatar da cewa ta kasance gwamnati ta-gari, mai kula da al’ummarta da kare su daga fadawa cikin rashin tsaro da kuma cire musu tsoro da samar musu da abubuwan more jin dadin rayuwa. Kenan irin wannan gwamnati ita ce ake kira da gwamnatin jin dadin al’umma, gwamnati da ke damuwa da halin da al’ummarta ke ciki a duk rana ta Allah. Duk fadi-tashin irin wannan gwamnati na neman mafita ne daga halin da al’ummar kasar suka samu kan su; kama daga tsarin mulki da siyasa da tattalin arziki da sauran batutuwan jin dadin rayuwa.
Irin wannan gwamnati ita ce ake kira da Ingilishi ‘Welfare state’, gwamnatin dadada wa al’umma. Gwamnati da masana suka nuna cewa tana shiga cikin rauhin rayuwar al’ummarta domin su san cewa suna da mai kula da su a duk rana ta Allah. Gwamnati ce da aka gina bisa tsarin samar da kyawawan al’amurran jin dadin rayuwa. Wato ke nan kamar yadda tsarin mulkin Nijeriya ya tanada, kamata ya yi a ce gwamnatin Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ta tanadi matakan da za ta bi domin ganin ta inganta zaman rayuwar al’ummar da take wa shugabanci. Amma tambayar da nake yi wa kaina a kullum ita ce, shin lallai wannan gwamnati ta san da wannan sashe na tsarin mulki da ya tanadi da ta tsare rayuka, ta cire tsoro, ta kuma samar da abubuwan  more rayuwa ga ilahirin al’ummarta?
Da yake ba ni ne Shugaba Jonathan ba, ba kuma ni ne mai ba shi shawara kan harkokin watsa labarai ko wani na kusa da shi ba, ba zan iya ba da amsa kai tsaye ba. Abin da zan yi shi ne in dora gwamnatin bisa silkelin da masana suka tanada na fahimtar ko gwamnatin na bisa turbar gaskiya ko kuma ta sanya giyar ribas ne wajen mulkin nata.
Shin gwamnatin Jonathan na kare rayukan al’ummar kasar nan kuwa? Mu dubi rayukan da aka rasa ta fuskoki da dama tun daga lokacin da ta hau mulki zuwa yau. Rayuka nawa aka rasa daga hannun ‘yan fashi da makami ko daga rikice-rikicen addini da na kabilanci? Nawa aka turbude daga hayaniyar ‘yan boko haram da ta Ombatse da ‘yan sara-suka da ‘yan daukar amarya da masu satar jama’a da kashe su don tsafe-tsafe? Shin aukuwar wadannan na nuna mana cewa akwai tsaro daga gwamnatin Jonathan? Shin wannan ba alama ba ce da ke nuna cewa jama’a yanzu na zama cikin tsoro ne, maimakon cikin tsaro? Shin fargaba da rashin zaman lafiya ba shi ne ke kai-kawo a tsakanin al’umma ba a fadin kasar nan? To wai ina sashin tsarin mulki da ya ce a kare lafiya da rayukan al’umma? kila an cire wannan sashe daga cikin tsarin mulkin Nijeriya da wannan gwamnati ke jagoranta ne!
Haka kuma wani bangare na tsarin mulkin da na ga kamar an yi watsi da shi, shi ne na daidaita rayuwar al’umma, a mayar da al’umma ta koma tamkar ‘ya’yan gurguzu, bai daya. Abin da aka yi wa Kudu, a yi wa Arewa, abin da aka yi wa Musulmi, a yi wa Kirista ko wanda bai da addini. A yi wa yaro da babba, a yi wa mace, a yi wa namiji. Ba bambanci! Amma shin hakan ne ke faruwa a cikin kasar a halin da muke ciki yanzu? Idan da gwamnati ta kokarta daidaitawa tsakanin al’umma da kila ba mu kasance cikin halin da muke ciki ba! dan Kudu na kyamar dan Arewa. Musulmi na nesa-nesa da Kirista ko wanda bai da addini. Igbo na kyamar Ijaw da sauran al’ummar Kudu-maso-Kudu. Yarbawa na ganin Hausawa a matsayin ci-ma-zaune ko kaskoki. Hausawa su kuma suna ganin wadanda ba Hausa-Fulani ba, a matsayin baki. Maganar daidaito tuni ta kau, ana ta yakin juna cikin ruwan sanyi. A wannan badakala ina gwamnatin Jonathan, kuma me take yi?
Saboda haka idan muka ce gwamnatin yanzu wadda Jonathan ke shugabanta ta gaza, ba wai don ba a son ta ba ne, sai dai don ta ki yin abin da ya dace a dube ta a matsayin gwamnatin kowa da kowa, ba ta ‘yan kalilan ba, musamman masu tursasa wa talaka!
Gwamnatin da dukiyar kasa ba ta kasa ba ce, ta wasu ‘yan kalilan ce daga al’ummar kasar, ba gwamnati ba ce! Gwamnatin da ta kasa samar da al’amurran kare lafiyar al’ummarta, ai ba gwamnati ba ce! Gwamnatin da dukkan sassan gudanar da ilimin ‘ya’yanta ya durkushe, ba ta damu ba, ba ta kula ba, wannan ba gwamnati ba ce! Gwamnatin da talauci ya yi katutu tsakanin al’ummarta, wasu kuma ‘yan kalilan na kwance cikin tafkunan arziki, ba gwamnati ba ce! Ina mafita? Amsar na wuyan al’ummar kasar nan baki daya idan sun yi wa kan su kiyamul laili, sun gane cewa su ne ke bayar da damar da ake yi musu sakiyar da ba ruwa. Lokaci ya yi kuma da za a gaya wa wanzami cewa, sakiyar nan ko da ta ruwa ce ta ishi talaka haka nan. Mu gani a kasa ko a yi waje-rod!