Me ke cikin suna?

A zamanta na ranar Laraba 24 ga watan Agustan bana, Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta sake tado da rikicin siyasar da ke tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Sanata Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon Mataimakinsa kuma Gwamna mai ci  Dokta Abdullahi Umar Ganduje, lokacin da ta zartar da kudurin  cewa gwamnatin ta cire tare da […]

Me ke cikin suna?
Me ke cikin suna?

A zamanta na ranar Laraba 24 ga watan Agustan bana, Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta sake tado da rikicin siyasar da ke tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Sanata Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon Mataimakinsa kuma Gwamna mai ci  Dokta Abdullahi Umar Ganduje, lokacin da ta zartar da kudurin  cewa gwamnatin ta cire tare da share duk inda aka rubuta sunan Kwankwasiyya ko Gandujiyya a kan duk gine-ginen gwamnatin jihar.
 kudurin da masu kula da al’amuran da ka je su komo a jihar ta Kano suke kallon Majalisar Dokokin ta zartar da shi ne a kan tsohon Gwamnan Jihar Sanata Rabi’u Kwankwaso da ya bi birni da karkarar jihar wajen rubuta KWANKWASIYYA a dukkan ayyukan da gwamnatinsa ta yi.
Honorabul Baffa Babba dan’agundi, Wakilin mazabar Birnin Kano da kewaye a Majalisar, shi ya kawo  kudurin a wancan zama na Majalisar Dokokin, har ma ya kara da a gaggauuta canja sunayen rukunin gidajen nan da gwamnatin Sanata Kwankwaso ta gina ta kuma sa musu sunayen biranen Bandarawo da Amana da Kwankwasiyya zuwa sunayen shahararrun malaman addini  wato marigayi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara da Sheikh Isiyaka Rabi’u, Shugaban darikar Tijjaniyya ta Afirka ta Yamma da kuma marigayi Sheikh Ja‘afar Mahmud Adam.
kudurin da tuni gwamnatin Dokta Ganduje ta yi na’am da shi, domin kawo yanzu rahotanni sun tabbatar da cewa an fara aikin goge sunayen a gine-ginen da al’amarin ya shafa.    
 Tun bayan da Sanata Kwankwaso ya yi ta maza wajen kasancewa shi ne Gwamnan jiha na biyu, tunda aka fara mulkin dimokuradiyya a  1999, a kasar nan, ya mika wa Mataimakinsa takarar neman mukamin Gwamnan Jiha da niyyar ya gaje shi, bayan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, yanzu kuma Sanata Alhaji Ahmed Sani Yariman Bakura da ya mika wa Mataimakinsa Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi ragamar mulkin jihar a shekarar 2007, bayan sun kammala wa’adin mulkin zango na biyu a shekarar.
Masu bin diddigin harkokin siyasar kasar nan, bisa ga la’akari da irin yadda Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura da Gwamna Mahmud Shinkafi ba su kare lafiya ba a cikin shekara hudu na wa’adin farko na Gwamna Shinkafi da kuma irin yadda a Jihar Kwara ba a kare lafiya ba tsakanin tsohon Gwamnan Jihar, yanzu kuma Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da mahaifinsa marigayi Sanata Abubakar Saraki da kuma irin yadda aka rabu dutse a hannun-riga tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Adamu Aleiro da wanda ya mika wa mulki a shekarar 2007, Alhaji Usman Nasamu dakingari da sauran inda aka yi irin waccan siyasar nadi, haka suka yi hasashen cewa ba za a kare lafiya ba tsakanin Sanata Kwankwaso da Gwamna Ganduje.
 Masanan, sun ce babban abin da ke kawo waccan sabawa da ke da wahalar shawo kanta, bai wuce irin yadda wadanda suka yi mulki ko suka taimaka wajen dora mai mulki, suke kokarin su dawo su yi kane-kane a cikin harkokin gwamnatin da suka sauka ba.  
Kamar yadda Gwamna Ganduje ya yi zargi a kwanakin baya, cewa tun daga lokacin nada masu mukaman siyasa a jihar, suka fara samun takun saka shi da Sanata Kwankwaso a kan ba a ba magoya bayan shi (Kwankwason)  mukamai ba. Kodayake jiga-jigan Jam’iyyar APC din biyu da suke fara haduwa a cikin tafiyar inuwar siyasar Jam’iyyar PDP, tun farkon kafuwarta a 1998, da dadi ba dadi suka ci gaba da zama tare, har zuwa shekarar 2014, da suka taimaka aka kafa sabuwar jam’iyyar APC, suka kuma koma cikinta su da magoya bayansu suka bar jam’iyyarsu ta PDP.
Cece-kuce da sa-in-sar da ta fito da wancan rashin jituwar jiga-jigan siyasar Jihar Kanon biyu karara ita ce ta watan Maris din da ya gabata, a lokacin da mahaifiyar Gwamna Ganduje ta rasu a kauyensu na Gannduje, shi kuma Sanata Kwankwaso ya je yi masa ygaisuwa a rana ta uku. A lokacin waccan ziyarar ta’aziiya ce aka yi zargin cewa wadansu magoya bayan Sanata Kwankwaso, da suka yi masa rakiya, sun yi  ta hargowa da hayaniya da furta kalamai na cin mutunci a kan Gwamna Ganduje da gwamnatinsa, tare da barazanar ba za su sake lamunce masa ya yi takarar neman wa’adin zango na biyu ba a shekarar 2019, in Allah Ya kai mu, bisa ga abin da suka kira gazawar gwamnatinsa na ta dora a kan akidar Kwankwasiyya, akidar da suka ce a kanta aka zabi Gwamna Ganduje a matsayin Gwamnan Jihar Kano a zaben 2015. Sai dai na kusa da Sanata Kwankwaso sun karyata tare da nesanta jagoransu da wadancan ayyukan assha.
In ban da abin ka da siyasar kasar nan da kuma wannan zamanin, me ke cikin suna? Abin da nake nufi da wannan tambaya shi ne wa ya ce aikin da wata gwamnati ko Gwamna ya yi sai an rubuta sunansa sannan ’yan kasa za su san cewa ga wanda ya yi su. Alal misali tunda na taso na ga manyan ayyukan ci gaba da shugabannin farko na kasar nan, musamman namu na Arewa irin su Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Jihar Arewa na farko kuma na karshe da gwamnatinsa ta gina.  Irin su rusasshen  Bankin Arewa wato Bank of the North da Kamfanin Bunkasa Ci gaban Arewa, wato NNDC da Kamfanin Siminti na Arewa da ke Sakkwato da Gidan Rediyo da Talabijin na Arewa (BCNN), da a yau ake kira Rediyon Tarayya na Kaduna da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da Kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo da Madaba’ar Gaskiya da ke Zariya, baya ga gine-ginen makarantu manya da kanana da hanyoyi da suka hada sassa daban-daban da asibitoci da matatun ruwan sha da sauransu.
Daga cikin irin wadannan ayyukan ci gaba Jami’ar Ahmadu Bello Zariya kadai ake ambatonta da sunan Sa Ahmadu Bello, ga shi kuma ’ya’yanmu ma a yau san sun cewa irin wadancan ayyukan raya kasa gwamnatin Sardaunan ta yi su.
Ba ma gwamnatin Arewa ba, hatta En-e, En-e na tsofaffin lardunan Arewa da aka yi, sun taka gagarumar rawa wajen samar da ayyukan ci gaban al’ummominsu da ake ambaton shugabannin wancan lokacin da su suka gina su irin su makarantun sakandare da asibitoci da hanyoyin karkara da makamantan su.
Alal misali a Jihar Kano En-e-En-en Kano ta Sarki Abdullahi Bayero ita ta fara gina tashar filin jirgin sama da matatar ruwa ta Chalawa. A dai Jihar Kano gwamnatin marigayi Kwamishinan ’Yan sandan Alhaji Audu Bako, daga cikin ayyukan raya kasar da ta yi sun hada da gina gidan gwamnatin da Gidan Murtala da Sakatariyar Audu Bako  da Sakatariya da Dam din Tiga inda ake da makeken filin noman ranin nan da ba irinsa a dukkan fadin kasar nan a yau.
Masu rura wannan wutar siyasa tsakanin Gwamna Ganduje da Sanata Rabi‘u Kwankwaso da makamantansu a sauran jihohi da kasa, lallai su kwana da sanin cewa irin wannan husuma ba abin da za ta tsinana musu, sai ma ta cutar da su. Kodayake masu magana kan ce wai siyasa kasuwar bukata ce, kuma ba ta da masoyi ko makiyi na dindindin, sai dai bukata ta dindindin, amma dai ba wani abu a cikin suna, aikin duk da wani ya yi, ya fi karfin wanda bai yi ba a ce shi ya yi.