Me ke damun Dokta Ahmad Gumi ne? (1)

A wannan karon, MALAM SHERIFF ALMUHAJIR, mai adireshin I-mel: [email protected] na Jami’ar Uniberisiti Sains Islam Malaysia ne muka mika wa filin, inda shi kuma ya kalubalanci Shaihin Malamin Islama, Dokta Ahmad Gumi, musamman game da takaddamarsa da dan takarar shugabancin kasa, a tutar APC, Janar Muhammadu Buhari. Ga abin da Almuhajjir yake cewa: Babu shakka […]

Me ke damun Dokta Ahmad Gumi ne? (1)
Me ke damun Dokta Ahmad Gumi ne? (1)

A wannan karon, MALAM SHERIFF ALMUHAJIR, mai adireshin I-mel: [email protected] na Jami’ar Uniberisiti Sains Islam Malaysia ne muka mika wa filin, inda shi kuma ya kalubalanci Shaihin Malamin Islama, Dokta Ahmad Gumi, musamman game da takaddamarsa da dan takarar shugabancin kasa, a tutar APC, Janar Muhammadu Buhari. Ga abin da Almuhajjir yake cewa:

Babu shakka addinin  Musulunci na da mahanga daban-daban a kan mulki na demokuradiyya, musamman irin wannan namu na Najeriya, sannan kuma wasu daga cikin malamai sun nuna cewa bai hallata ba amma ka’ida a kan fatawa ita ce; manyan masana addini a kowane yanki, su ke da alhakin duba fatawowi, lura da yanayin al-umma da kuma hanyoyin da suka fi cancanta da maslaha a cikinta.
Sakamakon haka, a tarihin wannan kasa an samu fitattun malamai na kowane bangare da suka ba da gudunmawarsu ta shawarwari da kuma nusantar da al’umma a kan yadda ya dace su mu’amalanci siyasar kasarmu Najeriya. Misali, kamar su marigayi Sheikh Abubakar Gumi, Sheikh dahiru Bauchi da kuma Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam. Dukkan wadannan kowa ya ba da tasa gudunmawa a kan halalcin shiga wannan siyasa da kuma hanyoyin da Musulmi zai bi don ya kauce wa halakar da kansa ko al’ummarsa ko addininsa.
Cikin ’yan kwanakin nan ma Dokta Ahmad Abubakar Gumi ya zo da nasa ra’ayoyi a kan siyasa kuma ya kawo fuskokin daban-daban a kan iya fahimtarsa. Cikin abun da ya zo da shi, akwai cewa tsakanin Shugaban kasa mai ci da kuma daya daga cikin ’yan takara na wannan lokacin, Janar Buhari, babu wanda ya cancanci jan ragamar al’ummar Najeriya kuma ya kawo dalilai daban-daban. Amma sai dukkan jam’iyyun suka yi watsi da shawararsa, suka fidda wadannan mutane a matsayin ’yan takara.
Dokta kuma ya ci gaba da suka irin ta siyasa ga Janar Buhari da magoya bayansa. Da ma can dai ya taba zargin shi Buharin da magoya bayansa da rashin tawakkali, sakamakon karar da shi Janar din ya shigar, yana kalubalantar zaben da ya gabata a 2007.
Wannan takarda tawa, na rubuta ta ne saboda nazari ga kalaman Dokta Gumi da kuma tasirin da za su iya haifarwa ga siyasar Najeriya.
A zahirin gaskiya, idan muka lura da yanayin Najeriya karkashin mulkin Jonathan tsawon shekara shida, za mu ga cewa ita wannan kasa baki dayanta ta samu ci baya ta dukkan bangarorin more rayuwa da hauhawar rashawa da cin hanci da kuma amfani da jami’an tsaro wajen tauye hakkin al’ummah. Baya ga rashin tsaro da ya halaka dubban mutane da ba a taba halakawa irinsu ba a tarihin kasar nan. Duk da kasar gaba daya ta cutu, amma yankin Arewa, inda kuma shi Dokta Gumi ya fito ya fi kowane yanki shan wahalar wannan gwamnati. Kuma babu shakka idan aka ci gaba da wannan gwamnati ta cika shekara goma kan mulki, to da mai amincewa da mai hanawa kowa sai ya dandana kudarsa.
Abun mamaki shi ne, shi Dokta yana zuwa da wasu kalamai da suke nuna cewa babu alheri a tattare da shi wannan dan takara daya tilo da jam’iyyar adawa ta tsayar, duk da cewa yana kuma nuna rashin amincewarsa da shugaban mai ci, amma kuma hankali kan iya nuna cewa hakan wata kofa ce yake budewa ta rarraba kan al’ummah da kuma rage musu azama a kan zaben wanda ke kalubalantar wannan gwamnati mai ci. Ya bar mabiya a dimauce tsakanin ko su saba masa, su zabi Buhari, ko su tsaya kada su yi zaben; mutanen Kudu su zabi nasu ya zarce, ko kuma su zabi shugaban mai ci, ganin za a zo da kudade don a saye imaninsu yadda aka saba.
Jaridar Leadership ta ruwaito Sheikh Gumi na gaya wa kungiyar Ibo cewa:
“Babu hurumi ga duk wani tsohon soja da ya yi juyin mulki a baya da zai yi korafi don an yi masa magudin zabe a shekara mai zuwa ta 2015.”
Wannan magana ta shi ba za ta samu karbuwa ba a hankalce kuma tana nuna zahirin cewa yana ba da dama ne ga gwamnati mai ci, wadda ita ke da dukiya da karfin soji, da ta murgude zabe. Kuma daga baya idan an kai kara ya dawo yana ce wa al’umma ba su da tawakkali. Wannan rashin adalci ne ga Janar Buhari saboda ko Alhaji Shehu Shagari ya tabbatar cewa ba Buhari ne ya yi masa juyin mulki ba, illa ma shi Buharin na gefe, dauko shi aka yi aka danka masa kasar. Kuma da shi Dokta zai yi amfani da wannan damar da ya samu ya kira gwamnati da su tabbatar da an yi ingantaccen zabe, shi ya fi dacewa da matsayinsa na babban malami, ba ya zuga gwamnati cewa ta yi magudin zabe ba.
Sannann Dokta Ahmad ya ce bayan ya yi kira ga rashin cancantar Buhari da Jonathan duka, masoya Buhari na aika masa da sakon barazana ga rayuwarsa. Wannan kazafi ne da yake neman ya kawo hujja a kan hakan, sannan kuma da hujjar da ke tabbatar da cewa wannan masoyin Buhari ne ya aiko. Abin da zai fi bayyana a wannan magana tasa ita ce; wani salo ne na bayyana wa duniya da kuma shagube na cewa mabiya Buhari ’yan ta’adda ne kuma su ne za su zub da jini su hana kasar zaman lafiya. Idan gaskiya za a bi, ta yaya ya gane cewa masoya Buhari ne suka yi masa sakon? Me ya sa bai zargi ’yan Jonathan ba?
Dokta Gumi ya rbuta a shafinsa na sadarwa cewa: “Nasihar da na yi wa Janar Buhari na kasancewarsa daya daga cikin shugabanin Musulmi tare da mabiyansa gaba daya ne, kakkashin wannan hadisi.”
Ni kuwa na ce, kun ga dai a nan ya bayyana zahiri da sunan Musulunci da shugabancin Musulunci ake wannan magana. To, mene ne manufar addini a kan zabe idan ana maganar addini? Ya kamata Dokta ya sani, da yawa daga masoya Buhari suna kaunar shi ne a kan nagartarsa, ba a kan addininsa ba kuma cikin mabiyansa akwai wadanda ba Musulmi ba. Duk da haka, a matsayinsa na malamin addini, ai ya san matsayar addini a kan zabe irin wannan mai zuwa.