Me ke faruwa a Matatar Dangote?

Yanzu shekaru 20 matatun man fetur na Gwamnatin Tarayya ba sa aiki

Me ke faruwa a Matatar Dangote?

’Yan kwanakin nan mun ji hayaniya ta cika Nijeriya a kan Matatar Man Fetur da Alhaji Aliko Dangote ya kafa domin sauwaka wa ’yan Nijeriya wahalhalun da suke ta fama da su a wannan kasa tamu.

Da farko kamata ya yi mu duba ire-iren wahalhalun da Nijeriya take fuskanta shekaru da dama tun lokacin soja har zuwa lokacin da fararen hula suka karbi mulki a 1979 da kuma a 1999.

Gaskiya tarihi ya nuna cewa Nijeriya tana da matatun man fetur da dangoginsa a Fatakwal, Kaduna da Warri.

A Fatakwal an ce akwai guda biyu, sannan a Warri da Kaduna akwai guda daidai, ka ga guda hudu ke nan ko kuwa?

Mu dauka muna da hudu ke nan cif. A hudun nan yau shekaru wajen 20 ke nan ba sa aiki. Mene ne dalilin haka?

Babu wanda har gobe zai fada mana dalilin rufe su, domin kawai cewa aka yi sun baci, kuma duk da cewa wurare ne, na samun kudaden shiga, amma an kasa gyara su, saboda bukatar wasu ’yan tsirarun mutane wadanda suke samun kudade masu kaurin gaske daga rashin aikin nasu.

Kuma an ce yawancinsu manyan ma’aikatan wuraren ne da masu harkar mai.

Kowa ya san cewa da gangan aka lalata injunan wurin, domin kawai sakaci da sakarci, wannan shi ne gaskiyar lamari, kuma za a fahimci cewa ita gwamnati tun daga na soji har zuwa na farar hula kamar ba ta damu da abubuwan da suke faruwa ba ne.

Tunda akwai zargin cewa, ana samun awalaja ce a tace man namu a waje da kuma dakonsa zuwa waje da dawo da shi duk wannan lamari ne daga manyan kasa!

An ce akwai lokacin wani farfesa kuma minista a wancan lokaci da ya bai wa mahukunta gwamnatin soja na lokaci shawara cewa maimakon jigilar man fetur da jiragen ruwa na haya, don me ba za a sayo jiragen da za su rika kawo man fetur din daga kasashen waje ba?

Ka ga ita gwamnatin wancan lokaci ba ta dauki shawarar ba, wato ta sayo wa Nijeriya jiragen jigilar tattaccen man ba.

To ka ga daga nan aka tabbatar da cewa zargin da ake yi ya fito fili cewa wasu manyan kasa ne ke bukatar haka ya ci gaba da tafiya a karkace, kuma yau shekaru da dama komai ya lalace kuma har gobe matatun man Nijeriya suna nan a lalace babu ranar gyaransu sai yaumat tanadi ke nan ko?

Abin sha’awa shi ne misalin da ake bugawa ga matatun mai na kasashen Ghana da Senegal, kusan tare muka yi da su kuma su daidai suke da su, mu kuwa Nijeriya muna da guda hudu, amma nasu suna nan kalau, namu kuma sun kasance a lalace shekaru aru-aru.

Kuma an ki gyarawa saboda wasu shafaffu da mai wadanda suke hana ruwa gudu. Kai don Allah wacce irin kasa muke da ita ce?

Kawai an zuba ido Nijeriya sai baya-baya take yi a kullum, koyaushe kuma duk mai son kasar ta gyaru sai kawai a sa masa wata kalma zargagungun?

Wai shin mene ne dalilin tsayuwar hakar man fetur a Bauchi da Gombe ne?

Na san dai tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya je ya bude wurin, amma shiru kake ji, an tsaya cak babu ko cewa me ya faru?

Ka ga ko lokacin marigayi Shehu Usman Shagari haka aka tsayar da na Jihar Borno har kawo yau din nan ba a sake ambato wurin ba – kai wannan abu dame ya yi kama?

Gaskiya dole shugabannin su tashi tsaye kususan na Arewa, domin akwai lauje a cikin nadi, ya zama dole a farka ba kawai rikicin shirme ba na ’yan siyasar Arewa da suke handame komai, suke haddasa mana rigingimu na babu gaira babu dalili domin raina mana hankali.

Ya zame mana dole mu farka daga barci domin kawo alheri ga jama’a.

Yanzu dai kuna gani ana neman a shamu da basilla game da Matatar Mai ta Dangote wacce za a iya samun man fetur da gas mai rahusa, kuma a yau wasu ’yan ta- kife daga cikin gwamnati suna neman lalata lamarin samun wannan rahusa, wadda Allah Ya daukaka bisa taskar arzikinSa.

Muna fada wa ko wane ne mutum, kuma komai matsayinsa, kada ya lalata wannan kyakkyawar niyya ta wannan bawan Allah, Alhaji Aliko Dangote.

Muna sane da kulle-kullen da ake yi domin kada talakawan Nijeriya su samu sa’ida, kuma hana arziki ga mai shi wahalar tsiya.

Kai dan Arewa wanda ba ka kaunar Arewa ahir dinka! Dole a bar Dangote ya kyautata wa talakawan Nijeriya.

Muna fata Dangote idan komai lafa ya samu kawo irin wannan matata a Arewa.

Kwamared Ibrahim Abdu Zango.

Shugaban Kano Unity Forum, Kano, Nijeriya 08175472298

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa