Me ke faruwa da jarumin fim RMD?

A ’yan kwanakin nan ne aka yi ta baza rade-radin cewa fitaccen jarumin fina-finan Turanci da ke Kudancin Najeriya, Richard Mofe Damijo ba ya da lafiya, inda ma har aka yi ta watsa hotunansa a kafafen sadarwar intanet a matsayin ramamme, domin tabbatar da cewa lallai yana fama da rashin lafiya.Kamar yadda mujallar NET ta […]

Me ke faruwa da jarumin fim RMD?
Me ke faruwa da jarumin fim RMD?

Daga hagu Richard Mofe Damij a yanzu, a daga kuma, lokacin da yake ganiyar tasheA ’yan kwanakin nan ne aka yi ta baza rade-radin cewa fitaccen jarumin fina-finan Turanci da ke Kudancin Najeriya, Richard Mofe Damijo ba ya da lafiya, inda ma har aka yi ta watsa hotunansa a kafafen sadarwar intanet a matsayin ramamme, domin tabbatar da cewa lallai yana fama da rashin lafiya.
Kamar yadda mujallar NET ta ruwaito labarin rashin lafiyar dan wasan, wanda a halin yanzu dan siyasa ne a Jihar Delta, ta tayar da hankalin masoyansa da kuma abokan sana’arsa.
Kamar yadda binciken Aminiya ya nuna, jita-jita ta yi ta bazuwa cewa dan wasan ma ya mutu, sai daga bisani ne aka tabbatar da cewa labarin ba gaskiya ba ne. Labarin ya faro ne tun lokacin da aka ga batun a turakar wata ’yar fim, Stella Damasus, inda aka kwarmata cewa: “daya daga cikin shahararrun ’yan fim din Nollywood kuma dan uwa, Richard Mofe Damijo a yanzu haka yana fama da wata rashin nlafiya mai tsoratarwa, wacce ana tsoron za ta iya zama sanadiyyar ajalinsa.” Bayan wannan sanarwa, an kuma lika hotunansa guda biyu, daya yana cikin walwala da koshin lafiya, daya kuma yana cikin damuwa kuma ga shi nan duk ya yamutse.
Ganin yadda wannan jita-jita ta zama kamar wutar daji da bazara, dan wasan da aka fi sani da lakanin ‘RMD’ ya tattauna da jaridar banguard, inda ya ce duk labarun da ake yadawa karya ne, hoton da ake gani cewa ya rame ba wani abu ba ne, ya zabi ya canja salon rayuwarsa ne, inda ya dauki matakan rage kiba. Daga nan ya gargadi jama’a da kuma ’yan jarida da su daina yada wannan labari.
“Shin me kuke bukata ne da ni kuma? Kun gan ni a dandali, na yi kama da mara lafiya? Wasu makiya ba su son ganin yadda jikina ya canja cikin koshin lafiya, don haka suka shiga ruruta labarin wai ba ni da lafiya kuma sun san labarin karya ne. Ni ina cikin koshin lafiya kuma jikina ya kara daukar siffa mai kyau fiye da lokacin da nake cikin kuruciya.” Inji RMD.
A halin yanzu dai dan wasan ya tsagaita fitowa cikin fina-finai, domin shi ne Kwamishinan Al’adu Da Al’amuran Shakatawa na Jihar Delta. A kwanakin baya ne ma aka ba shi kambin karramawa saboda gudunmowar da ya bayar a harkar fina-finai.
Kafin ya hau mukamin Kwamishina a jiharsa ta haihuwa, dan wasan ya fito cikin fina-finai sama da hamsin, cikinsu har da wani mai taken biolated wanda Amaka Igwe ya shirya.