Me komawar Mbappe Real Madrid ke nufi ga ci gaban kungiyar?
Idan Modric ya bar Real Madrid a karshen kakar bana, Mbappe zai karbi riga mai lamba 10.
Yanzu dai za a iya cewa an yi ta, ta kare bayan dan wasan gaban kungiyar PSG da tawagar Faransa, Kylian Mbappe ya amince zai koma taka leda a kungiyar Real Madrid ta Spain idan an kammala kakar bana.
Mbappe mai shekara 25 ya sanar da PSG cewar zai bar kungiyar da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen kakar watan Yuni.
- Kasashe 10 da aka fi dauke wutar lantarki a Afirka
- Yadda Dalar Amurka ke jefa ’yan Nijeriya cikin kunci
Mbappe ya bukaci a fayyace makomarsa kafin watan Maris, wanda ya tattauna da Shugaban PSG, Nasser Al-Khelaifi ranar 13 ga watan Fabrairu da cewar yana son komawa Real Madrid.
Bayan sanin cewar Mbappe na son barin kungiyar tun ranar Alhamis ta makon jiya, hakan ya sa ba a fara saka shi ba a wasan gasar Ligue 1 ranar Asabar a wasa da Nantes.
Daga baya ya shiga karawar, inda ya ci kwallo a bugun fenariti, tuni PSG ta bayar da tazarar maki 14 a kan teburin Ligue 1.
An ce ana sa ran zai amince da kunshin yarjejeniyar kaka biyar da zai ke karbar albashin £12.8m a kowace kakar tamaula.
Haka kuma Real Madrid za ta bai wa Mbappe £128m kudin rattaba hannu a kwantiragi da ladan wasa da sauransu da za a biya cikin shekara tara – sannan zai rika karbar kashi na tallace-tallacensa.
Tuni kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya fara tunanin wurin da zai ke saka Mbappe tare da Jude Bellingham da kuma Binicius Junior.
Idan kuma Luka Modric ya bar Real Madrid a karshen kakar bana, Mbappe ne zai karbi riga mai lamba 10, irin lambar da yake sa wa a PSG.
Rahotanni na nuna cewa, tun a watan Janairu ne dan wasan da Real Madrid suke tattaunawa domin samun matsaya a kan albashinsa da sauran abubuwa.
Sai dai alamu sun nuna cewa, dan wasan zai rage albashin da yake karba ne a kungiyar PSG domin cika burinsa na zuwa Real Madrid din.
Sai dai suma kungiyar ta Madrid za ta sake masa mara wajen karbar kudaden tallacetallace, domin daidaita shi da albashin Bellingham da Vinicious Jnr. Idan ya hada da kudaden talla, zai fi su samun kudi sosai.
Idan ba a manta ba, tun a bara ne Real Madrid ta yi zawarcin matashin dan wasan mai shekara 25, a kan kudi Dala miliyan 130, amma PSG ta ki amincewa, inda ta kekashe kasa cewa lallai dole dan wasan ya ci gaba da zama a kungiyar domin ya kara musu kwantiraginsu.
Sai dai bayan an wuce wannan, kungiyar ta kara masa kudi, sannan ta bukaci ya tsawaita kwantiraginsa, kasancewar a watan Yunin bana ne zai kare, shi ma nan ya ce ya ki.
Tun a kakar bara PSG ta san cewa kwantiraginsa zai kare ne a bana, kuma idan bai sabunta ba, a kyauta zai bar kungiyar, wanda wasu masu sharhi a kan harkokin wasanni suke gani kamar ba daidai ba ne, a ce matashin dan wasan, da a yanzu ake ganin tauroronsa ya fi haskawa ya bar kungiyar a matsayin kyauta.
A kungiyar PSG, Mbappe ya zura kwallo 244, sannan ya taimaka an zura kwallo 93, sannan ya lashe kofi Gasar Ligue 1 sau biyar.
A kakar bara da dan wasan ya nuna sha’awarsa ta tafiya, sai da ya samu matsala da kungiyar, inda har kungiyar Al Hilal ta Saudiyya ta yi masa tayin kwantiragin Dala miliyan 259 da ba a taba yin irinsa ba a harkar tamaula a duniya, amma ya nuna cewa shi Real Madrid kawai yake so.
Idan Mbappe ya dawo Madrid, zai hadu da zaratan matasan ’yan wasa irin su Bellingham, wanda shi ne yanzu yake daukar kungiyar, da Vinicious Jnr da Rodrigo da sauransu.
Wasu masana harkar kwallon kafa suna ganin jiran Mbappe ne ya sa Real Madrid ta dauko aron dan wasan gaba Joselu domin ya rike wajen kafin Mbappe ya zo.
Daga zuwan Jude Bellingham a kakar bara daga kungiyar Dortmund a kan Dala miliyan 134 zuwa yanzu, ya taka wasa 21, inda ya zura kwallo 16.
Kusan duk wasa, hankalin magoya bayan kungiyar hankalinsu kan shi yake komawa domin samun sakamako mai kyau.
Sai dai wata matsalar ita ce ana tunanin dole a sauya wa Bellingham waje a filin wasan Real Madrid domin barin Mbappe ya wataya.
Tuni kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya fara tunanin yadda zai sauya tsarin ’yan wasa 11 na kungiyar domin kada zuwansa ya hana wani dan kwallon nuna bajintarsu.
Ana tunanin dole Bellingham ya dan dawo baya, ya rika wasa a gaban ’yan wasan tsakiya, sannan a tura Mbappe gaba, amma ya fi kusa da gefen hagu, domin dan wasan bayan ba ya son zama a gaba kawai, wato ainihin lamba tara.
Sai dai shin akwai wani sabon abu da kungiyar ke bukata? A kakar bana, wasa biyu aka doke Real Madrid, kuma duka biyun Atletico Madrid ne ta doke ta.
Kungiyar ce a saman teburin Laliga, kuma ta samu nasara a dukkan wasanninta na Gasar Zakarun Turai.
Wannan ke nufin ko dai Bellingham ya sauko baya, ko kuma ya koma can gaba, sai a saka Binicious a gefen dama, Mbappe a hagu, Bellingham a gaba, idan za a yi amfani da ’yan wasan gaba uku, wanda ke nufin Rodrigo ya koma benci.
Sai dai ana tunanin hakan zai rage wa Bellingham karsashi wajen cigaba da tashen da yake yi saboda sauyin waje a filin.
Sai dai kamar yadda aka yi zamanin, Benzema, Bale da Cristiano Ronaldo, lokacin da Real Madrid ta zama kungiyar farko da ta zura kwallo 100 a kaka daya a kakar 2011-2012 a karkashin koci Jose Mourinho, inda kungiyar ta samu kwallo 121 a kaka daya, wanda ya haura tarihin da kungiyar take da shi na zura kwallo 107 a kakar 1989-1990, ana tunanin idan wadannan matasan ’yan wasan suka watsatsake, za su iya fin wadancan zaratan ’yan wasan.
Haka kuma a tsakiya, kungiyar yanzu ta tara matasan ’yan wasa, masu jini a jika, wadanda ake tunanin za a dade ana yi da su duba da yanayin shekarunsu, irin su Tchoumani da Camavinga da Diaz da Militao da sauransu, kungiyar Real Madrid za a iya cewa tana gina da kungiya mai karfi da nan gaba kadan za su fitini kowa a duniya.