Me kuke so in fada game da auren Fatima Ganduje?- Sheikh Daurawa

Shugaban Hukumar HISBA, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi bayani a karon farko a kan auren diyar Gwamnan Jihar Kano, Fatima Ganduje. Shi dai wannan biki, wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu suka jagoranta a Kano, ya samu halartar gwamnoni da manyan kasa, sannan kuma an yi shagulgula da yawa wanda wasu […]

Me kuke so in fada game da auren Fatima Ganduje?- Sheikh Daurawa

Shugaban Hukumar HISBA, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi bayani a karon farko a kan auren diyar Gwamnan Jihar Kano, Fatima Ganduje.

Shi dai wannan biki, wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu suka jagoranta a Kano, ya samu halartar gwamnoni da manyan kasa, sannan kuma an yi shagulgula da yawa wanda wasu suke ganin bai kamata ba.

Mutane suntan tambaya wai ina HISBA take ne ake ta irin wannan biki a Kano.

A cewar Shehim malamin kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito daga shafinsa na facebook, “A ranar Asabar na tafi Jihar Sakkwato da misalin karfe daya na rana jim kadan bayan an kammala daurin auren domin in halarci taron kaddamar da littafin sharhin Iziyya da Dokta Mansur ya wallafa.

“Bayan na yi kwana biyu a Sakkwato, sai na tafi Zamfara domin yin wa’azi, na yi  kwana daya a can sai kuma na tafi Kaduna domin gabatar da shiri a gidan Talabijin na DITV na sa’a biyu.

“A ranar Juma’a sai na yi wamata wa’azi a garin Rigasa da ke Kaduna, sannan kuma na yi hudubar juma’a, sannan kuma bayan sallar Magriba sai na yi wa’azi a masallacin marigayi Sheikh Rabiu Daura.

“Da safiyar Asabar sai na kara yi wa wasu matan wa’azi a masallacin Sultan Bello daga nan kuma sai dao Kano. Duk wanda ke son gani na, yanzu na dawo ofis dina.

“Kowa na so ya ji jawabina a kan bikin auren diyar gwamna, me kuke so in fada?