Me ya kawo ka-ce-na-ce kan aurar da ‘ya’yan Musulmi?
Al’amuran da suka biyo bayan muhawarar da aka tattafka a majalisar dattijai, da kuma irin tataburzar da ta wakana yayin amincewa ko yin watsi da shawarar kayyade shekaru mafi karanci don aurar da ‘ya’ya mata suna da ban takaici, musamman ma saboda ganin cewa an nemi a wuce gona da iri, a kuma ci wa […]
Al’amuran da suka biyo bayan muhawarar da aka tattafka a majalisar dattijai, da kuma irin tataburzar da ta wakana yayin amincewa ko yin watsi da shawarar kayyade shekaru mafi karanci don aurar da ‘ya’ya mata suna da ban takaici, musamman ma saboda ganin cewa an nemi a wuce gona da iri, a kuma ci wa Musulmin kasar nan da addinin da suka yi imani da shi fuska. Tun da farko dai ba wannan batun ne ba aka takalo a zauren Majalisar dattijan amma sai ga shi nan an sarko wannan maganar ta kayyade adadin shekarun ‘ya’ya mata kafin su yi aure.
Abu kamar wasa sai ga kungiyoyin addini da kuma masu rajin kare hakkin bil-adama da ‘yan siyasa da masu sha’awar tayar da husuma don gogawa addinin Musulunci kashin kashi sun shiga tijara da terere game da haka, suka yi ta aikawa da sakwannin batanci ga jama’ar duniya baki daya ta kafafen sadarwa ta yanar gizo, suna kuma kira da kakausar murya lallai a kokarta wajen dakile abin da suka kira muguwar dabi’ar Musulmin Najeriya. A nan cikin gida kuma jaridu, musamman ma na kudanci, wadanda suke jiran kyas su shiga sana’arsu ta muzgunawa Musulmi, sun dukufa ka’in da na’in wajen yin sharhi da da’awar tozarta Musulmi da abubuwan da suka yi imani da su bisa tsarin addininsu da kuma umurnin Mahaliccinsu.
Abin takaici game da haka shi ne ganin yadda wadannan mutane suka yi ta cin karensu ba babbaka, babu wanda ya kwabe su don a kwantar da ran jama’ar da suka rigaya suka bakantawa. Amma idan da su ne aka yi wa haka da sama da kasa za su hade, kuma hatta kasashen Yahudu da Nasara za su shiga cikin wannan baragadar don taimakawa wajen cin fuskar Musulmin Najeriya. Wannan ba abin mamaki ba ne domin kuwa irin wannan mummunan al’amari ya samo asali ne daga kasashen ketare, wadanda suka mayar da addinin Musulunci abokin gabarsu, babu gairan ba dan dalili, sai dai don muguwar aniyarsu ta raba kan jama’a don tara abin duniya.
A yanzu ‘yan Najeriya sun dade da fahimtar cewa bambance-bambancen addini da na kabilanci sun zauna da gindinsu, dirshanshan, kuma babu wata ma’amala da za a yi ba tare da an yi la’akari da yadda za su yi tasiri ba a cikin harkokin siyasa da na zamantakewa. Ana yin haka ne kuwa don a mayar da wasu saniyar ware, a dakile burinsu na more dukkan ‘yancin da suke da shi na ‘yan kasa, a kuma hana su yin ibadarsu daidai da yadda yake a cikin littafin da Mahaliccinsu ya saukar masu ko kuma bisa ka’idojin da ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin kasarsu. Ta haka ne aka bullo da wasu dabaru a 1999 don hana Musulmi bin tsarin shari’ar Musulunci wacce su kadai ta shafa, ba ruwan abokan zamansu da ita, balle a ce za ta yi aiki a kansu.
Amma duk da haka nan sai da aka zuga su, suka tayar da kayar baya, suka nuna kwakkwarar adawar da ta jawo yamutsin da ya yi sanadiyyar asarar dimbin rayuka da dukiya. An yi haka ne kuwa domin a farraka kawunan Musulmin Arewacin kasar nan da abokan zamansu mabiya Almasihu, an kuma samu gagarumar nasarar domin kuwa a yanzu haka babu yadda za a yi Musulmi ya amince da Kirista a wasu harkoki, musamman ma a zabe, haka nan kuma Kirista ba zai amince ya zabi Musulmi ba. Inda wannan batu ya yi tasiri shi ne a zaben shugaban kasa da aka yi a 2011, yayin da yawancin Kiristocin Arewa suka dangwala wa Shugaba Jonathan, Musulmin kuma suka jefa wa Janar Buhari.
Ashe ke nan ba domin komai ne ba ‘yan Kudu da wasu ‘yan Arewa ke ta dora wa Janar Buhari karan-tsana, ake kyamatarsa, ake tozarta shi, sai don kasancewarsa dan Arewa, kuma Musulmi, kar ka dada, kar ka rage. Amma shugabannin siyasa da na addini a Arewa sun kasa fahimtar haka, balle su dauki matakan magance matsalar. Gobe idan wani can daga Arewa, kuma Musulmi, daban da Buhari, zai fito neman takarar Shugabancin kasa sai an yi wasan kura da shi fiye da yadda aka takura wa Janar Buhari. A yanzu ma manyan ‘yan siyasan Arewa ba su da wata akida sai ta bin tafarkin yadda za a muzguna wa Musulunci, idan kuwa ba haka ba to kashinsu zai bushe.
Ashe ke nan wannan batancin da aka dukufa yi wa Musulmi game da wa’adin shekarun aurar da ‘ya’yansu mata abu ne da ya dace da manufofin ‘yan kudancin da ke koyon dabi’un Yahudu da Nasara don kara dulmuya Musulmi cikin koramar kiyayyar da suke nuna masu, ba ma a nan Najeriya ba, har ma a ko ina a duniyar nan. Wannan al’amari na aurar da ‘ya’ya mata ba sabon abu ne ba a duniyar Musulunci, kuma idan har Yahudu da Nasara na son kawo karshensa to sai su fara daga kasar babbar aminiyarsu, wato Saudiyya, inda addinin Musuluncin ya samo asali. Idan kuma ba za su iya ba sai su rufa mana baki.