Me ya rage a takarar Buhari?
daya da daya idan ka ce tunda aka dawo da harkokin mulkin dimokuradiyyar kasar nan yau shekaru 16, ba a taba gudanar da sahihi, kuma karbabben zaben fitar da gwani ba a dukkan jam`iyyun kasar nan irin wanda aka yi a jam`iyyar APC tsakanin ranakun Laraba da Alhamins din makon da ya gabata a Ikko,wanda […]
daya da daya idan ka ce tunda aka dawo da harkokin mulkin dimokuradiyyar kasar nan yau shekaru 16, ba a taba gudanar da sahihi, kuma karbabben zaben fitar da gwani ba a dukkan jam`iyyun kasar nan irin wanda aka yi a jam`iyyar APC tsakanin ranakun Laraba da Alhamins din makon da ya gabata a Ikko,wanda ya tabbatar da nasarar tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya zama dan takarar neman shugabancin kasar nan a a inuwar jam`iyyar tasu don zaben shekara maizuwa, to, kuwa ba wanda zai ce karya ka yi. Kama daga fitowar`yan takara da yadda aka bari kowannensu ya nemi jama`a, aka kuma ba su zabin kodai su yi masalaha a junansu ko kuma inmasalahar ta gaggara to, a je zabe wakilai na kasa su raba musu gardama. Bayan masalaha ta gagara aka kuma tafi zaben aka kuma yi zaben da dukkan `yan takara da `yan kwarakonsu (wadanda suka yi nasarar da wadanda ba su ba) kowa ya ce ya gamsu. Sabanin zabubbuka irin wadannan da suka gabata wadanda tun daga kansu ake tafi zaben kasa kai a rarrabe.
A wancan zabe, wanda Janar Buhari ya lashe da gagarumin rinjaye, inda ya tashi da kuri`u 3,430, daga cikin kuri`u 6008, da wakilan taron da suka fito daga jihohin kasar nan 36 da Abuja babban birnin tarayya suka kada. Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso da ya zo na biyu ya tashi da kuri`u 974, ya yin da tsohon Mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya zo na uku, da kuri`u 954, Gwamnan Jihar Imo Cif Rochas Okorocha ya samu kuri`u 624, inda ya zo na hudu, yayin da Mawallafin rukunin jaridun Leadership Mista Sam Nda Isaia ya zo na biyar ya samu kuri`u 10.
Ba wai yadda tsarin gudanar da zabubbukan suka gudana ba ne kadai abin burgewa da sha`awa ga masu yi wa jam`iyyar ta APC fatan samun nasara ba, a`a babban abin burgewar shi ne irin yadda shugabancin jam`iyyar ya bude kofa ya kuma samar da yanayi kyakykyawa ga kowane dan takarar har ya samu cimma burinsa na ya tsaya takara a cikin jama`iyyar da ransa ya kwanta masa kuma daga karshe ya gamsu da sakamakon da yasa mu na nasara ko akasi. Alkawarin da dukkan `yan takara suka yi tun kafin aje zaben fitar da dan takarar neman shugabancin kasar da bayan bayyana sakamakon zaben, shi ne kowannensu zai ba da gudummuwar da yake ita ce don samun nasararar jam`iyyar a babban zaben da za a yin ita ma wata babbar nasara ce ga jam`iyyar da ke fatan a wannan karon ta karbi mulki a shekara mai zuwa. Samuwar hakan ba wani abu yake nuni da shi ba, sai irin shirin da jam`iyyun adawa na rusassun jam`iyyun adawa (ANPP da ACN da CPC da wani bangare APGA da wasu gwamnonin PDP) da suka hade wuri daya suka kafa sabuwar jam`iyyar APC a shekarar da ta gabata da aniyar lallai sai sun karbi mulki daga jam`iyyar PDP mai ikirarin za ta mallaki kasar nan har nan da shekaru 60.
Yanzu tun an kai ga wannan fage kuma Allah cikin ikonSa, ya amsa rokon dimbin miliyoyin `yan kasar nan da suka dade suna addu`ar daukar tutar takarar ga Janar Muhammadu Buhari, to kuwa akwai manya-manyan kalubale da shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam`iyyar ta APC za su yi shirin fuskanta. Na daya ina fata zuwa yanzu an kawo karshen dambarwar zaben wanda zai kasance Mataimaki ga Janar Buhari a wannan takara Allah Ya sanya wanda aka zaba ya zama karbabbe ga mafi yawan `yan kasa wanda yake da kishin kasa da halayen dattijantaka sannan kuma mai ra`ayin a ciza a hura, don tabbatar da gaskiya da adalci.
Akwai kuma bukatar tun tafiya ba ta yi nisa ba, dukkan wadanda suka fafata da Janar Buhari a cikin takarar neman shugabancin kasar su hudu da wadanda suke ba da gagarumar gudummuwa cikin tafiyar baki dayanta tun yanzu a tabbatar musu da irin mukaman da za a ba su ko mutanensu. Samuwar haka a wannan lokaci zai ba su damar mika wuya a yi da su yadda ya kamata sai inda karfinsu da na aljihoonsu ya kare, tunda an riga an kwadaita musu nasu kason. Wata babbar magana a wannan tafiya ta Janar Buhari ita ce tsare amana lallai akwai bukatar tabbatar da cewa manya da kananan `yan jam`iyya, musamman masu ruwa da tsaki ba su shiga cikin wata kunbiya-kunbiya da jam`iyyar adawa ta PDP ba da aniyarsu taimaka wa dan takararta koda na dan Majalisar Dokoki na jiha ne a mazabunsu da sunan su huce haushin ba nasu aka tsayar ba. Lallai akwai bukatar dukkan shugabanni da iyaye da masu ruwa da tsaki da magoya baya da masoyan jam`iyyar APC, kowa ya tsaya akan akidar “APC SAK” a cikin wannan babban zabe don kuwa an ce kishin BAkI sai taro.
Zuwa yanzu cikin ikon Allah yekuwar da wasu `yan adawa suka rinka yi a shekarun bayan na cewa idan Janar Buhari ya zama shugaban kasa zai mayar da kasar nan mai bin tafarkin shari`ar Musulunci yanzu ta zama tarihi, don kuwa da yawa yanzu sun gane cewa farfaganda ce kawai irin ta siyasar kasar nan wadancan mutane suka yi. Lokaci da aka dauka Janar Buhari yana gwagwarmayar yaki da zalunci da neman a tsaida gaskiya da adalci a cikin kasar nan ta sanya a yau ba sai gobe ba tsohon shugaban kasa Janar Olusegun Obasanjo, na cikin masu fadin gaskiya da cancantar Janar Buhari ya shugabanci kasar nan duk kuwa da shi Janar Buhari bai taba sassautawa tsarin da bai yiwakasa dadi ba a mulkin Cif Obasanjo.
Daga irin halin da ake ciki akwai bukatar jama`ar kasa a ci gaba da dagewa da addu`o`in Allah Ya ba mu ikon zaben shugabanni na gari. Ya raba mu da `yan gangan da `yan ganganci, masu son su mulkemu ta kowane hali; Ya sa mu zabi wadanda za su kawo mana zaman lafiya kwanciyar hankali karuwar arziki, amin summa amin.