…Me ya sa aka tuhume ta da raba kan jama’a?
Sai dai duk da kokarinta wajen neman ’yancin bakaken fata an tuhumi marigayiya Winnie Mandela da gudanar da bakin mulkin a yankunan birnin Soweto. Wadansu mambobin Jam’iyyar ANC sun raba gari da ita bayan ta amince da a rika kona wadanda ba su goyon bayan fafutikar da take jagoranta. An same ta da laifin yin […]

Sai dai duk da kokarinta wajen neman ’yancin bakaken fata an tuhumi marigayiya Winnie Mandela da gudanar da bakin mulkin a yankunan birnin Soweto. Wadansu mambobin Jam’iyyar ANC sun raba gari da ita bayan ta amince da a rika kona wadanda ba su goyon bayan fafutikar da take jagoranta.
An same ta da laifin yin garkuwa da kuma kashe wani yaro mai shekara 14, mai suna Stompie Seipei. Amma ta sha musanta wannan tuhuma.
Mandela ya goyi bayanta a lokacin da take fuskantar wadannan tuhume-tuhume Amma shekara biyu bayan sake shi daga kurkuku a 1996 sai aurensu ya mutu. Amma ta ci gaba da amfani da sunansa har bayan mutuwarsa.