Me ya sa ake musayar yawu tsakanin APC da PDP?

Su waɗanda ke waɗannan zarge-zargen suna ƙoƙarin ɗauke hankalin gwamnati daga kan ayyukan da take aiwatarwa.

Me ya sa ake musayar yawu tsakanin APC da PDP?

Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin babban zaben 2027, ana ci gaba da musayar yawu kan shirye-shiryen manyan ‘yan siyasa da ke hamayya da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda suke tarurruka tare da tuntuɓar juna kan yadda za su kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027.

Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani kan kalaman da wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyun adawa da na cikin gidanta suke yi, inda suka zarge ta da sauka daga kan turbar da jam’iyyar take.

Fadar Shugaban kasa na mayar da martani ne bayan wani taro da jagororin hamayya da wasu daga cikin ‘yan Jam’iyyar APC da ke adawa da gwamnatin suka gudanar a Abuja.

Jam’iyyar ta APC dai ta ce hakan ba komai ba ne illa yunƙurin da masu adawa da gwamnatin ta Bola Ahmed Tinubu ke yi na kawar da hankalin Tinubu daga hidimar da yake wa al’ummar kasar nan.

Sai dai Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce, borin kunya ce gwamnatin APC ke yi, saboda manuniya ta nuna cewar al’ummar kasar nan sun gaji da mulkinta.

Malam Abdul’aziz Abdul’aziz na ɗaya daga cikin masu magana da yawun Shugaban kasar ya bayyana cewa, ganin irin rawar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ke takawa wajen gyara kurakuran da Jam’iyyar PDP ta yi ne tsawon shekara 16 da suka ɗauka.

“Suna mulki ne ya sa suke kaɗa gangar siyasa tun kafin lokacin ya zo.

“Su wadanda suke irin wadannan zarge-zargen ai su ne mutanen da suke ɗauke hankalin gwamnati daga kan abin da ya kamata ta yi”, in ji Abdul’aziz.

Shi kuwa mataimakin mai magana da yawun Jam’iyyar PDP, Alhaji Ibrahim Abdullahi ya ce, martanin na fadar shugaban ba komai ba ne illa shure-shure da baya hana mutuwa, wanda duk ya iske shinkafa a Naira 6,000 da PDP ta faɗi zabe, yanzu kuma yake sayen shinkafar nan kan Naira 100,000, lallai akwai ayar tambaya da ake cewa wai ana gyara a cewar Ibrahim.

Fadar shugaban ta ce, taron da suka gudanar ba komai ba ne illa na wadanda ba sa fatan ci gaban kasar nan da kuma son tunzura al’umma da barazana da kuma bayyana ra’ayoyin da za su durƙusar da dimokuradiyya.

Jam’iyyun hamayya na fama da rikice-rikicen cikin gida, lamarin da masana kan harkokin siyasa ke bayyanawa da cewa zai iya kawo musu tarnaƙi wajen haɗewar da suke niyyar yi.

A shekarar 2023 ce dai Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi nasarar doke Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP a Zaɓen Shugaban kasa, inda aka samu wasu gwamnonin PDP da ake zargin sun yi wa Jam’iyyar APC aiki.

Yanzu dai hankali ya karkata ne wajen ganin irin wainar da za a toya a babban taron Jam’iyyar PDP, wadda ke kan gaba a sahun jam’iyyun adawa.

 

HOTUNA: Abba ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano

’Yan bindiga sun kashe fasto a Gombe

An shiga nuna wa juna yatsa tsakanin Hamas da Isra’ila

Dalilin da na ziyarci Obasanjo — Atiku