Me ya sa ake ta kokawa? (2)

Ba dabashirin da ya dace a irin wannan harkalla sai a natsu a fahimci tsarin da shi ne mafita ta alheri. A gane me ya kamata a dauka, me ya kamata a watsar, me ya kamata a yi, me ya kamata a bari! Da zarar aka cimma wannan manufa sai kuma a zauna domin aiwatarwa. […]

Me ya sa ake ta kokawa? (2)

Ba dabashirin da ya dace a irin wannan harkalla sai a natsu a fahimci tsarin da shi ne mafita ta alheri. A gane me ya kamata a dauka, me ya kamata a watsar, me ya kamata a yi, me ya kamata a bari! Da zarar aka cimma wannan manufa sai kuma a zauna domin aiwatarwa. Ya dace wajen aiwatarwa a san ina ne iyaka ta irin halin da ake ciki, ana kuma yi ana yin tambayoyi da neman amsa! Shin jama’a na cikin tasku har yanzu ko kuwa an fitar da su daga kunci? Idan suna nan kamar jiya i yau, me ya dace a yi don sama musu mafita? Idan kuma an samu nasara a wasu sassa na gudanar da rayuwa to ya dace a bayyana, daga masu gudanar da lamurran da kuma wadanda ake yi domin su. Yin haka zai sa a san inda ake da inda aka nufa, da ma kuma an san in da aka fito can baya.

Irin wannan yanayi shi ne ke sa ake samun yarda da amincewa da daidaituwar tunani tsakanin masu mulki da wadanda ake mulka. Sai dai a kula duk inda aka samu akasin haka to tambayoyi da korafe-korafe ba su daina yin aringizo daga wadanda ake mulka ba, haka kuma, in ba a samu amsa daga bakin da ya dace ba, to ba abin da ake yi sai saka da zaren da bai da amfani.

Shi ya sa ko a wannan sharhi ba abin da muka mayar da hankali irin tunkudo tambayoyi daga hawan dutsen damuwar da al’umma take ciki, kuma ba yadda za a yi a hana mutane yin tambayiyi da kuma kokawa. Shin a irin halin da ake ciki an kuwa samar wa al’ummar da suka zabi canji, canjin da suka zuba cikin aljihu domin shiga kasuwa don sayen abin masarufi? Wasu za su ce daga cikin manyan bangarori uku na alkawurran da masu shara da tsintsiya suka yi na awon gaba da su, wato kawo karshen ta’addanci irin na boko haram da na ‘yan Neja Delta da kuma tsagerun kasar Yarbawa da kuma kawo karshen sata da cin hanci da rashawa da almundahana a cikin kasa da kuma tabbatar da an tayar da komadar tattalin arzikin kasa ta mayar da hankali wajen samar da sababbin kafafen shigowar kudi a cikin kasa; wasu sai sambarka, wasu kuma sai madalla-tir! Ba sai an fada ba, boko haram da ta’addanci a Neja Delta da tsageranci a kasashen Yarbawa sun fara gane hanyar mutuwa, lokaci kawai ake jira. Amma kuma ba laifi ba ne in mutane suka koka kan cewa a daidai lokacin da ake kan godaben shawo kan matsalar ta’addancin da aka gada daga gwamnatin Jonathan, wasu masu kama da su na ta bullowa. Ina maganar satar mutane da garkuwa da su? Ina sababbin hanyoyin fashi da makami da rikice-rikice na addini da kabilanci da na makiyaya da manoma? Shin don an rangada ta’addancin boko haram da ire-ire sa a kasa, wasu sababbin sun bulla sai a hana mutane kokawa? Ba za a hana ba, ba kuma laifi ba ne. Abin da ya dace a yi shi ne a koma bisa teburin neman mafita ga wadannan sababbin matsaloli, a shafe ido a fito da sababbin hanyoyin magance su. A lura, ba ranar da kasa mai neman shiga dakin ci gaba irin Najeriya za ta daina cin karo da sababbin matsaloli, ke nan ba ranar da mutane za su daina kokawa dangane da ire-iren wadannan matsaloli.

Haka batun yake dangane da sata da cin hanci da rashawa da almundahana a cikin kasar nan. An yi damalmala da kudaden al’umma, na gani-da-fada a zamanin Jonathan, amma shin an daina damalmalar irin wannan a halin yanzu a zamanin mulkin Buhari? Shin ma’aikata sun daina sata da cin hanci ko kuma rashawa? Shin an daina zurmuken kwangila da makamantan su? Shin kasafin kudin Najeriya ana yin sa yadda ya kamata ko ana aiwatar da shi yadda ya dace? Idan akwai matsaloli, shin bai kamata a tattauna su ba? Bai dace a ce mutane sun koka ba in sun ga gwamnati ta fara shirin amazaya, a koma zamanin Jonathan? Shin kokawa irin wannan laifi ne?

 

Za Mu Ci Gaba