Me ya sa ake ta kokawa? (3)

Ba sai an nanata ba, lallai an yi damalmala da kudaden al’umma, na gani-da-fada a zamanin Jonathan, amma tambayar ita ce, shin an daina damalmalar irin waccan a halin yanzu a zamanin mulkin Shugaba Buhari? Shin ma’aikata sun daina sata da cin hanci ko kuma rashawa? Shin an daina zurmuken kwangila da makamantan su? Shin […]

Me ya sa ake ta kokawa? (3)

Ba sai an nanata ba, lallai an yi damalmala da kudaden al’umma, na gani-da-fada a zamanin Jonathan, amma tambayar ita ce, shin an daina damalmalar irin waccan a halin yanzu a zamanin mulkin Shugaba Buhari? Shin ma’aikata sun daina sata da cin hanci ko kuma rashawa? Shin an daina zurmuken kwangila da makamantan su? Shin kasafin kudin Nijeriya ana yin sa yadda ya kamata ko ana aiwatar da shi yadda ya dace? Idan akwai matsaloli, shin bai kamata a tattauna su ba? Haka kuma shin bai dace ba a ce mutane sun koka in sun ga gwamnati ta fara shirin amazaya, a koma zamanin Jonathan? Shin kokawa irin wannan da wasu ke yi, laifi ne?

A ganina kokawa in an ga abin da ba daidai ba daga wani bangare na al’umma ba laifi ba ne, abin da tsarin dimokuradiyya ya gada ke nan. Kila abin da wasu za su tambaya shi ne, ai ba gwamnati ce kadai za ta canza lamurra ba, su kan su talakawa ya dace a ce suna kokarin canza lamurra, domin ba Shugaba Buhari ba ne ministoci ko gwamnoni ko ’yan majalisar tarayya ko shugabannin kananan hukumomi; idan sun lalace bai dace a dora laifin ga Shugaba Buhari ba. Fadin haka ba daidai ba ne, domin da na gaba ake gane zurfin ruwa, haka kuma shi kifi in ya tashi lalacewa daga ka yake nuna alamu. Ke nan dukkan irin tabargazar da wasu za su yi a cikin wannan yanayi, laifin na ga wanda ya dauki gammo ya ce zai dauki dutsen Dala, domin kila ya hango matakin da zai bi ne ya dora dutsen a ka, shi ya, kuma kila ya san haryar da za bi ta kai shi gaci. Wannan ba yana nufin cewa duk wani laifi na gwamnatin Tarayya ba ne ko kuma na Shugaba Buhari, ko alama, amma kukan da wasu ke yi domin Shugaba Buhari ya ji ne, ya duba don gyara da kansa ko ya sa wasu su yi gyaran domin sa, in ba a yi gyaran ba kuma ya tabbatar an binciki dalilai, in an samu mai laifi a tsawata ko a hukunta, in na daurewa a daure, ta haka za a fahimci cewa aiki ake yi ba zaman dirshan ba.

Me nake so a fahimta a nan? Gyara ba na shugaba ba ne shi kadai, har da na masu kokawa, kila shi ma shugaban yana da damar ya koka in ya ga abubuwa sun ki tafiya yadda ya kamata, musamman in ya fahimci cewa matsalar ba daga shi ko mukarrabansa ba ne, daga talakawan ne da yake mulka, (wannan wani batu ne na daban). Saboda haka muna iya cewa kokawa ba ta talakawa ba ce kadai, shugaba ma na da damar ya koka. A takaice dai kokawa dole ne a cikin irin wannan tsari.

Abin da kawai yake damun al’umma a halin yanzu shi ne rashin sanin madafa, rashin sanin tabbas, rashin kalailaice inda za a da yadda za a tafi din. Shin akwai alamun haske a gaba game da halin da ake ciki a yau? Ko an tanadi baturin da zai haska fitilar kawo canjin? Idan ba a samu kwakkwarar amsa ba, to ya dace a koma kan tebur domin nazari. Ya dace a sake baje kolin tunani game da canjin da ake bukata a cikin kasa. A canza fasalin rawar da ake ta faman yi yanzu, tun da kidi ya canza ko kuma masu kallon rawar na ganin ba ta burge su ba. Dole ne shugabanni su kasance jarumai dangane da bin matakin ladabtar da masu neman bata wa gwamnati ko mulki suna ta kowace fuska. A cikin tafiya irin wannan dole ake samun nagari na na banza, amma ba na banza mafaka bisa kowace irin fuska kafa ce ta lalata tafiyar mulki. Haka su kuma wadanda ake mulka ya dace a nuna musu cewa ba sani-ba-sabo a mulki, abin da ya ci Doma ba zai bar Awai ba. A yi haka kuma da tunanin hanya ce zama abin godo da koyo. Idan har ana gyaran harkar ilimi ko gyaran makarantu, to a tabbata ana yin haka domin ’ya’yan shugabanni da talakawa. Haka gyaran hanyoyi da makamantan su. Duk lokacin da aka rarraba makarantun kasa suka zama na masu shi daban, na talakawa daban ko hanyoyin mota da jiragen kasa suka kasance na talakawa, su kuwa shugabanni na sama kamar tsuntsaye, ba abin da ake yi sai dasa tsiron turaddadi da damuwa a cikin kasa.

Daga karshe kokawa kadai daga talakawa da shugabanni ba shi ne mafita ba, dole a yi wa tsarin mulki garambawul, a tabbata an auna nasarar da aka samu da wadda aka iske don a bambanta duma da kabewa. Yin haka zai sa a san ina ne za a nufa. Idan har jiya ta fi yau dadi, komin irin kurarin da za a dinga yi na canji, ba mai kunnuwan ji, bare ya shiga jiki. Idan kuma jiki ya ki ya motsa, ba yadda za a yi a yi katabus a kowace tafiya.

Ta yaya za a cimma wannan kuduri? Hanyoyi uku masana falsafa suka tanada. Da farko mu yi komi da zuciya daya, wannan shi ne zai bude mana idanu mu gane gaskiya, gaskiya ce, domin bin ta. Na biyu, a tuna ba wani tsiro da zai rayu in ba a yin ban ruwa, ko dai daga ruwan sama ko kuma na kwalfin jigo. Sai dai kuma ba abin da ke sa tsiro ya yi yabanyar kwarai sai kulawa mai inganci. Saboda haka mu yi wa kowane irin kalubale turke na musamman, ta haka ne za su zama mana rakumi da akala, sai yadda muka yi da su. Idan mu da shugabanni muka yi wannan alkawari, muka mayar da kasar a matsayin uwa tagari, wadda za mu bauta wa yadda ya kamata, ba za mu taba gazawa ko jin kunya ba, domin kuwa Allah na tare da wanda ke taimakon kan sa!