Me ya sa Boko Haram ke hakon Gwamna Zulum?
A makonni biyu da suka gabata ne Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tsallake rijiya da baya a karo na uku bayan da ’yan bindigar da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai masa hari a lokacin da ya ziyarci garin Baga da ke Karamar Hukumar Kukawa, a kokarinsa na ganin mutanen […]
A makonni biyu da suka gabata ne Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tsallake rijiya da baya a karo na uku bayan da ’yan bindigar da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai masa hari a lokacin da ya ziyarci garin Baga da ke Karamar Hukumar Kukawa, a kokarinsa na ganin mutanen garin sun koma garinsu.
Jama’a da dama sun rika tofa albarkacin bakinsu kan hare-haren kwanton baunar da ake kai wa Gwamnan inda wadansu ke ganin akwai lauje a cikin nadi, yayin da wadansu suke ganin har yanzu babu tsaro a wuraren da Gwamnan yake kokarin an mayar da mutane garuruwansu.
- Gwamnoni 4 sun kaiwa Zulum ziyara jihar Borno
- Boko Haram: Gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya
- Zulum ya damka wa matar hafsan sojin da Boko Haram ta kashe N20m
A tsakiyar watan Yuli ne Gwamna Zulum ya fara kai ziyara garin Baga, bayan zuwansa Monguno, wanda a waccan tafiyar ce, bayan barin Mil Ninety sai ’yan bindigar da ake zargin na Boko Haram suka yi masa kwanton bauna suka auka wa ayarin Gwamnan, kuma duk da cewa babu asarar rai da aka samu, a wancan lokaci hakan ya kara sa shakku a zukatan jama’a kan yiwuwar komawar mutanen garuruwansu.
Duk da wancan hari da aka kai ga ayarin Gwamna Babagana Zulum maimakon ya yi kasa a gwiwa, sai ma ya kara kaimi don ganin cewa dukkan mutanen da Boko Haram ta kora, sun koma garuruwansu.
Gwamnan ya kafa kwamitin kwararru don tabbatar da ganin wannan kudiri ya samu nasara.
’Yan kwamitin sun samu gagarumar nasarar sake gina garin wanda a cewar shugaban kwamitin sun samu nasarar kusan kashi 85 na sake gina garin.
Kuma a ranar Juma’ar da ta gabata ce, Gwamna Zulum ya kaddamar da rukunin farko na komawa garin Baga, wanda shi da kansa ya jagoranci jami’ansa zuwa garin.
Sai dai wannan tafiya ta Gwamna Zulum ta sake haduwa da cikas a garin Cross (Kuros) Kauwa a yankin Monguno, inda tantancewar ta tafi yadda ya kamata, amma bayan ayarin Gwamna ya bar garin, kusa da Mil Nati, wajen da aka kai wa Gwamnan harin farko, aka sake kawo musu wani mummunan hari.
Kwamishinan Shari’a na Jihar, Alhaji Kaka Shehu a hirarsa da Sashin Hausa na BBC, ya ce suna cikin tafiya sai bama-bamai uku suka tashi, kuma daga tashinsu ’yan Boko Haram suka bude musu wuta, inda jami’an tsaron da ke tare da Gwamnan suka maida martani.
“Wannan ya yi sanadiyar mutuwar jami’an tsaronmu, sai dai Allah cikin ikonSa babu abin da ya samu Gwamnan,” inji shi.
Wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Maiduguri, Malam Aliyu Suleiman Abubakar, ya ce shirin Gwamna Zulum na mayar da mutane garuruwansu abu ne mai kyau.
Ya ce “Amma yaya lamarin tsaron yake? tunda ka ga shi kansa bai fi karfin a kai masa hari ba, to yaya ga jama’ar da suka koma garuruwansu?”
“Don haka ina ganin kamata ya yi gwamnati ta tabbatar da ingantaccen tsaro tukunna, wanda hakan zai taimaka sosai.”
Shi kuwa Malam Kabiru Usman cewa ya yi, harin da ake kai wa Gwamnan manuniya ce cewa akwai sauran aiki kan batun kawo karshen rashin tsaro, “Dole dukkanmu mu hada hannu ta yin addu’a da taimaka wa Gwamnan, don wannan ba aikinsa ba ne shi kadai.”
“Kuma ga duk mai hankali, hare- haren da aka kai wa Gwamnan a fil yake cewa shiryawa aka yi don dakile kokarinsa na samar da zaman lafiya.”
“Kuma ina da yakinin cewa wadannan hare-hare ba za su karya masa gwiwa ba, don na ji ya fada yanzu ya fara zuwa Baga, kuma zai sake zuwa Baga.”
Sannan a watan Oktoban nan za a maida mutanen Marte da Abadam da sauran ’yan gudun hijira zuwa garuruwansu,” inji shi.
Baba Ali Soja kwararre ne a harkar tsaro ya bayyana wa Aminiya cewa akwai manufunci a cikin lamarin.
“Ina fada maka ba hari za a kai wa Gwamna ba, a yadda na san Gwamna Zulum babu abin da zai sa ya ja baya kan yunkurinsa na maida jama’a garuruwansu.”
“A iyaka sanina kuma a matsayina na tsohon soja da na san yaki, ya kamata jami’an tsaronmu su tabbatar da ganin sun kara zage dantse da kara sa himma.”
“Ba wai na ce ba sa kokari ba ne, amma maganar gaskiya idan har Gwamna bai fi karfin a kai masa hari ba, to ina wanda ba ya da mukamin komai?”
“Gaskiya dole ne sojojinmu su canja tsari, don akwai alamomin tambaya kan yadda suke tafiyar da aikinsu.”
“Wani abu ko ba jami’in tsaro ba ne kai ka san akwai raini hankali.”
Ali Soja ya ce kokarin ganin ’yan gudun hijira sun koma garuruwansu, babban abin ci gaba ne ga yunkurin gwamnati na ganin an kawo karshen ayyukan ’yan ta’adda a yankin da kasar nan.