Me ya sa ICPC ta kama mawaki D’Banj?
Hukumar ta ce ta kama shi ne saboda damfara a shirin N-Power
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ta ce ta kama fitaccen mawaki Ayo Oyebanjo, wanda aka fi sani da D’Banj ne bisa zargin damfara da tsarin tallafin Gwamnatin Tarayya na N-Power.
Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Azuka Ohuhua, ta fitar, ICPC ta ce an kamo mawakin ne domin bincikensa kan badakalar shirin.
Azuka ta ce, “Mun samu korafin yadda wasu ke samun biliyoyin Naira da shirin, bayan wasu da suka rabauta sun ce ba sa samun kudadensu na karshen wata, duk da gwamnati na biya.
“Akalla mutum 10 muka gayyata ofishinmu kan laifukan da ke da alaka da hakan, kuma mun sallami wasu daga ciki.
“Mista Oyebanjo na hannunmu har yanzu, kuma yana shalkwatar ICPC tun ranar Talata yana taimakawa mana binciken da muke gudanarwa.
“Binciken zai kasance mai fadi, kuma za a mika shi ga sauran masu ruwa da tsaki a yaki da zamba cikin aminci, da kuma bankunan da wadanda suka ci gajiya suka bude asusu.