Me ya sa iyaye mata ke hana ’ya’yansu auren ’ya’yan talakawa?
Irin yadda iyaye, musamman mata, suke yin ruwa da tsaki wajen hure wa ’ya’yansu kunne, don su guji mazajen da suka fito neman aurensu, saboda kawai ba su da abin duniya, ya zama ruwan dare gama duniya a wannan zamani.Kodayake ba kasaifai iyaye mata suke iya cin galaba a kan ’ya’yansu maza ba, sai dai […]
Irin yadda iyaye, musamman mata, suke yin ruwa da tsaki wajen hure wa ’ya’yansu kunne, don su guji mazajen da suka fito neman aurensu, saboda kawai ba su da abin duniya, ya zama ruwan dare gama duniya a wannan zamani.
Kodayake ba kasaifai iyaye mata suke iya cin galaba a kan ’ya’yansu maza ba, sai dai sun fi yin tasiri a kan ’ya’yansu mata, saboda kusancin da suke da shi a gare su. Akasari shi namiji ya fi kusanci da mahaifinsa, ita kuwa ’ya mace ta fi kusanci da mahaifiyarta. To amma duk da haka, wadansu iyaye matan suka wuce gona da iri wajen hana ’ya’yansu mata auren talaka.
Dalilin da ya sa na ce haka shi ne irin haka ta faru a kan wani saurayi mai suna Ali Munkaila Madobi da budurwarsa Shamsiyya a Jihar Legas. A lokacin da ya fito neman aurenta yana sana’ar sayar da itace a unguwarsu Shamsiyya. Duk da dadewar da suka yi suna soyayya da ita har na tsawon shekaru da dama ba ta taba nuna cewa ba ta sonsa ba, sai daga bisani da mahaifiyarta ta ga lallai Ali da gaske yake wajen so ya auri ’yarta Shamsiyya, sai ta fito karara ta nuna adawarta da auren.
Da mahaifiyar ta ga lallai ya dage sai ya auri Shamsiyya duk da kiyayyar da take nuna masa, sai ta fito karara ta shaida masa cewa ’yarta ba za ta auri matsiyaci ba sai mai arziki. Har ta rika cewa ga masu arziki suna son su neme ta amma Ali ya hana su fitowa. Saboda haka ta kafe a kan cewa babu yadda za a yi ya auri ’yarta. Wani abin mamaki shi ne, duk da kaunar da mahaifin Shamsiyya yake yi wa Ali mahaifiyarta ta dage ba zai aure ta ba. Har daga bisani mahaifiyar ta samu sabani da majinta a kan batun, amma duk da haka duk da ranar auren da aka sanya ba a yi auren ba saboda daga bisani sai da mahaifiyarta ta samu nasara ta hure wa wa ’yarta kunne, har ta kai ta fito karara ta fadawa Ali bakaken maganganu. Kai daga bisani ta gaya masa cewa ba ta son sa kuma ba ta kaunarsa.
Abin da ya sa na kawo misali da wannan saurayi shi ne, yadda abin ya ba jama’ar yankin mamaki irin yadda zamani ya sauya har ta kai iyaye mata na fitowa karara su rika bayyana kwadayinsu ga dukiya. Wannan abu abin takaici ne da ya kamata iyayenmu mata su guje shi, kuma su yi nesa da shi. Su gane cewa arziki yin Allah ne ba dan Adam ba ne yake yi wa kansa.
Ba wai ina dora wa iyaye mata laifi ba kawai har da iyaye maza. Su ma ya kamata su ji tsoron Allah su guji hana ’ya’yansu maza auren ’ya’yan talakawa. Domin su ma ba su suka jawo wa kansu talaucin ba. Abin da ake bukata shi ne mutum ya yi aure saboda Allah ba don abin duniya ba. Kuma mutum ya zabi mace ta gari mai tarbiyya ba wacce za ta watsa masa gida ba, ta hana shi kwanciyar hankali.
Kada wasu su yi mini mummunar fahimta ba sukar masu arziki nake yi ba, kuma ba bata musu suna nake yi ba, kuma ba sukar ’ya’yansu nake yi ba. Ai ko ba komai arziki abin so ne, kuma talauci abin kyama ne, babu wanda yake son talauci. Su ma daga cikin masu arzikin akwai ’ya’yan mutunci da tarbiyya da ladabi da kuma biyyaya bila adadin. Kamar yadda a cikin talakawa akwai bata gari, haka ma a cikin masu arziki akwai baragurbi.
Za a iya tuntubar Abu Mujahid ta 08027406827