Me ya sa mata ke jure talaucin gidan iyayensu, ban da na mazajensu?
“Mace ba ta da zabi a kan iyayenta, amma miji kuwa za ta iya dirjewa ta zaba”
Bari mu fara da taken da mata ke yi wa talakan miji, inda suke danganta shi da tsohuwar mota; ga rashin dadi ga matsala – a duniya kuma ai babu wanda ke son matsala ko?
Mace ba ta da iko a kan zabin iyaye, duk yadda ta bude ido ta gansu, duk tsaurin idonta hakan za ta rike su a matsayin nata domin dai ba a sauya wa tuwo suna.
- Mece ce makomar siyasar Kwankwaso bayan ficewa daga PDP?
- An fara gyaran titin jirgin kasan da aka dasa wa bam a hanyar Kaduna
Baya ga hakan, tana tashi ne da yakinin zamanta a gidan uba na da wa’adi, ba kamar gidan miji da ake fatan daga nan sai kushewa ba, kuma duk yadda aurenta zai zo da jinkiri za ayi kuma za ta tafi, tana mai burin samun inda za ta fi samun yalwar inuwar hutawa.
A duk lokacin da mace ta bude ido ta ganta da auren talaka, ta kan jure ne kawai in har mijin yana bakin kokarinsa ta fannin kula, yana mai tausasa harshensa a kanta ko kuma babu yadda ta iya, bi ma’ana gidan talakan mijin nan shi ne Aljannar duniyarta.
Fadin rai
Ban fiye ganin laifin mata a kan rashin jure talaucin gidan aure ba saboda akasarin maza talakawa akan same su da fadin rai, wulakanci, magana mara dadi da tozarta mace, uwa uba kuma ga raina sana’a.
Sai a iske mai gida ya yi shekaru bai tanadar ma iyalinsa abin da za su ci ko suturce jiki ba, in suka yi magana ya bi su da zagi da bakar magana, in aka taimaka musu daga danginsu ya dinga tijarar an mayar da shi fakiri.
Shi bai fita ya yi kwadago ya samu taro da sisi ba, shi kuma bai natsu ya yarda cewa makomar arzikinsa na ga jajircewarsa a nema ba.
Da za a tsayar da shi a tambayi dalilin rashin yin wasu sana’o’in, nan za a ji fatawar ta fi karfin wasu ayyuka.
Don Allah ta yaya mace za ta jure tun da ban da talauci har da lalaci ga rashin daraja dan-Adam?
Butulci
Dalili na biyu kuma shi ne mata kan tsoraci jure talaucin gidan miji don gudun butulcin talakan da ya sami kudi.
Ya faru fiye da adadi mace ta yi hakuri ta jure talaucin miji, da dadi babu dadi, ba wanda zai ji, wani lokaci har ta yi sana’a don ta rufa masa asiri.
Amma daga ranar da ya samu arziki zai nemo matar cin arziki ba tare da ya tuna halaccin da matar ta yi masa ba, sai ma kara nuna mata kusancin ta da talauci da zai yi ta hanyar yin biris da bukatunta.
A karamin tunaninsa, ai ba ta san dadin arziki ba.
Wani mai karfin halin ma tikitin kammala aurensa zai yanka mata. Ya darje ya auri wacce za ta taya shi cin arzikin da ya yi.
A duk lokacin da suka tuna wannan sakamakon juriyar da mata kan dauka sai su botsare su gwammace a ce sun gaza hakuri da su yi a yi musu sakayya da wulakanci.
Dogon buri
Duk da rashin halaccin wasu maza, akwai matan da kuma dogon buri ya yi musu yawa, har hakan kan hana su jure babun miji.
Irin su za a iske ko da suke karkashin iyayensu sun rayu ne kawai don ba su da ikon sauya kalar rayuwar su.
A haka suke cin burin auren mai hali yadda ba za su wahala ba, idan aka yi rashin sa’a kuwa suka auri talaka, sai su gwammace a kirga musu aure da su yi wahalar banza.
Akwai matan da gasa tsakanin kawaye kan ja su, su gagara hakuri da aljihun mazajensu, ko da kuwa suna kokari ko suna lullube da rufin asirin Ubangiji.
Gidan uba kodayaushe abin alfahari ne, ba a sauya shi, a duk yadda yake sai sambarka ba kamar na miji ba.