Me ya sa Shugaba Buhari yake Sallah a kan kujera?

A ’yan kwanakin nan wasu hotuna da suka nuna Shugaba Muhammadu Buhari yana sallah a zaune a kan kujera sun jawo muhawara tare da ce-ce-kuce a kafafen sada zumunta na zamani a Najeriya. Muhawarar dai ta biyo bayan wallafa hotunan Shugaban Kasar ne yayin gudanar da sallar Idi da kuma sallar Juma’ar da ya gudanar […]

Me ya sa Shugaba Buhari yake Sallah a kan kujera?

Shugaba Buhari yayin gudanar da sallar Juma’a

A ’yan kwanakin nan wasu hotuna da suka nuna Shugaba Muhammadu Buhari yana sallah a zaune a kan kujera sun jawo muhawara tare da ce-ce-kuce a kafafen sada zumunta na zamani a Najeriya.

Muhawarar dai ta biyo bayan wallafa hotunan Shugaban Kasar ne yayin gudanar da sallar Idi da kuma sallar Juma’ar da ya gudanar ranar 5 ga watan Yuni a Masallacin Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

A yayin duka sallolin biyu, hotunan sun nuna Buhari yana sallar a zaune a kan kujera lokacin da Babban Limamin Masallacin Fadar Shugaban Kasar, Imam Abdul-Wahid Suleiman, yake jagoranci.

Ana ta tafka muhawara

A daya daga cikin irin ra’ayoyin da aka bayyana a shafin sada zumunta na Facebook na Aminiya, wata mai suna Rasheedat Abdallah ta ce: “Shin wai shi Buhari…me [hakan] ke nufi – sallar Idi na gan shi a kan kujera, still (har yanzu) Juma’a yana kan kujera?”

Aminu Abbas ma cewa ya yi, “A gaskiya wannan abin yana kulle min kai, a wajen sallar Idi na ga shugaban kasa a kan kujera a cikin masallaci a cikin sahu yana kan kujera, wai ina malamanmu ne?”

Ita kuwa Hauwa’u Ahmad Ahmad cewa ta yi, “May be (mai yiwuwa) yana da problem (matsala) ne na sunkuyo, ko ciwon baya ko kafa; ya halatta in ba za ka iya ruku’u ko sojood ba cikin sallah ka yi ta a haka ai, har a kwance ai ya halatta Musulmi ya yi sallah in dai akwai larura ko?”

Ko da yake wannan salon da shugaban kasar ya dauka na yin sallar ba wani sabon abu ba ne, watakila wadannan ’yan Najeriya na bayyana ra’ayoyin nasu ne saboda suna tsammanin ganin shi a tsaye.

Fadar Shugaban Kasa ta yi gum

To sai dai kokarin jin ta-bakin Fadar Shugaban Kasa a kan wannan lamari ya ci tura.

Da muka tuntubi Mai Magana da Yawun Shugaban Kasar Malam Garba Shehu don jin dalilin da ya sa shugaban kasar ke sallar a zaune a kan kujera ya ce ba shi da ta cewa a kan batun.

Shugaba Buhari yayin sauraron hudubar bayan sallar Idin karamar sallah a gida tare da iyalansa

Me Musulunci ya ce?

A wata tattaunawa da Aminiya a kan lamarin, wani malamin addinin Musulunci a birnin Abuja, Ustaz Maisuna M. Yahaya, ya ce shugaban na da damar ya yi sallarsa a zaune, ko a gida ko kuma a masallaci.

Ustaz Yahaya, wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar Musulmi ta Al-Mustofiyya ta Najeriya, ya ce yanayin da zai sa mutum ya yi sallah a zaune ya danganta da ikon mutum kamar yadda Shari’ar Musulunci ta tanadar.

“Idan mutum na da iko, ya yi sallah a tsaye, idan kuma ba zai iya ba sakamakon rashin lafiya, ko tsufa, ko gazawa, ko wasu dalilai, to sai ya yi a zaune a kan shimfida ko kuma a kujera”, inji malamin.

Ya kuma kara da cewa, “Amma idan yanayi ya sa ba zai iya yi a zaunen ba, to sai ya yi a kwance kan tsaginsa na dama, ko na hagu ko kuma a rigingine”.

Shi ma a tasa fatawar, Babban Limamin Masallacin Fouad Lababidi da ke Wuse a Abuja, Dakta Tajuddeen Bello Adigun, ya ce Buharin ba kuskure ya yi ba.

Ya ce Shari’ar Musulunci ta yi tanadin sauki ba tsanani ba ga mutane.

Ya kuma ce wadanda suke alakanta zaman na shugaban kasa yayin sallah da cewa hakan na nuna gazawarsa karara a harkokin jagoranci sun yi kuskure.

“Akwai dalilan da suke tilasta mutum ya yi sallah a zaune, ko dai a kan kujera ko kuma a kan shimfida, ko ma ya yi ta a kwance.

“Game da shekarun Shugaba [Buhari] yanzu haka, ’yan Najeriya sun san cewa ba matashi ba ne lokacin da suka zabe shi, [kuma] mun gan shi ya halarci taruka da dama, a wasu lokutan ma har ya tsaya sa’o’i da dama.

“Saboda haka alakanta yin sallarsa a zaune da nuna gazawarsa wajen jagoranci ba daidai ba ne kuma ba su ma da alaka”, inji Dakta Adigun.