Me ya sa soyayya ke komawa kiyayya, masoya ke zama abokan gaba? (4)

Ina kuke masu bibiyar wannan muhimmin shafin na Dausayin Kauna, a farfajiyar FDK? A yau mun shiga mako na hudu a wannan maudu’i da ke bin kadin yadda al’amuran soyayya ke rikidewa gaba tsakanin masoya maza da mata.  Ga sakon nin da suka samu shiga a wannan makon, sai a ci gaba da bibiyarmu da […]

Me ya sa soyayya ke komawa kiyayya, masoya ke zama abokan gaba? (4)

Ina kuke masu bibiyar wannan muhimmin shafin na Dausayin Kauna, a farfajiyar FDK? A yau mun shiga mako na hudu a wannan maudu’i da ke bin kadin yadda al’amuran soyayya ke rikidewa gaba tsakanin masoya maza da mata.  Ga sakon nin da suka samu shiga a wannan makon, sai a ci gaba da bibiyarmu da hakuri:

Sakon Anas Nuhu Rijiyar Lemo (07034312244) ya fado komar FDK, wanda yake cewa: “FDK, na fi kowa farin cikin kawo wannan maudu’i, wanda ke cike da rudani da abin mamaki. Sai ka ga saurayi da budurwa sun tabka soyayya abar koyi amma da zarar sun shiga ciki sai ka ji mummunan labari.

“Hakan na faruwa ne sakamakon soyayyar da suke wa junansu a iya fatar baki ko kuma saurayin ya yi mata karya a waje, idan an yi auren sai ta ga duk shifcin gizo ne; ko kuma rashin iya tsabta da magana da kuma kishi a kan abinda Allah ne Ya ce a yi (karin aure).

“A ganina, wadannan abubuwa na sa masoya su koma makiya ga junansu. Allah Ya ganar da mu, domin ni ma ina cikin wata cakwakiyar da Fatima S. Ibrahim amma ba mu kai ga aure ba.”

Shi kuma Abu Ubaida Rabi’u Kano, a nasa sakon yana cewa: “FDK, Ni a tuanina, abin da ya sa so yake komawa kiyyaya shi ne; gina soyyayar tun farko ba a kan gaskiya ba. Mutum zai ga mace wani abu a jikinta ya ja hankalinsa, daga ya samu abin nan shi ke nan kuma yawancin aure a kan so ake dora shi ba kauna ba. So yana gushewa amma kauna tana nan har abada.

“Abin da ya sa mata suke kashewa ko raunta mazansu, son zuciya ne. Idan dan uwansu zai kara aure sun fi kowa zumudi. Ita wadda za a kara wa auren ba mace ba ce, ba ta kishi? Amma idan a kansu ne sai hankalinsu ya gushe kuma yadawa da ke a gidajen rediyo ya taimaka wajen yaduwar laifin. Wata ba ta san ya za ta yi ba, ta ji wata ta yi ba a dau hukunci ba, ita ma sai ta gwada. Allah Ya shiryar da mu tafarkin gaskiya, Ya raba mu da son zuciya, amin.

Sai kuma sakon Usman Sa’idu Maiduguri (08033478055): “FDK, ni tawa shawarar ita ce, idan har ana so a samu zaman lafiya tsakanin ma’aurata shi ne, da zarar an yi aure to duk layukanta na waya ta rabu da su, ta karya su, ta nemi wani layin. Domin da zarar tana amfani da layinta, tsofin samarinta za su rika hira da ita. Daga nan sai ka ga suna hure mata kunne, daga nan sai a samu matsala.”

Safiyanu S. Nuhu Kano (08082262381): “FDK, a gaskiya na shiga cikin wannan matsar amma daga baya na gano matsar, na magance ta.

“1-Abin da ke kawo wannan matsar, rashin fahimtar juna 2-Kuma wasu matan ko mazan, girman kai da ba za su tsaya ba su tattauna matsarsu ba don su samu mafita. Gaskiya tsayawa tsakanin mata da miji su tattauna yana kawo fahimtar juna. Na gode, Allah Ya daukaka Aminiya da masoya Aminiya.”

Sai kuma sako daga hannun Rabilu Usman Yangemen Kankara Jihar Katsina, yana cewa: “Abin da ke kawo soyayya ke zama kiyayya, akwai rashin soyayya tsakani da Allah da kuma sa karya a cikin soyayya. Ba ma tsakanin saurayi da budurwa ba, har ma a biki da ba soyayya ta Allah sai in kana da abin hannu. Kai har ma ’yan uwa a yanzu ba soyayyar Allah da Annabi (SAW) ake yi ba, sai kana da abin hannu ake sonka. Soyayyar Allah ta yi karanci, sai dai Allah Ya kyauta, amin.”

Sai sako daga Fadima (08085862289), tana cewa: “Ni dai ina ganin cewa yin auren dole ne ke kawo haka amma da za a daina yawan haka da abin ya ragu.”

Shi kuwa Hafeez M. Sani Kofa Bebeji, cewa yake: “FDK, a gaskiya wannan babbar matsala ce da muke fama da ita a cikin al’ummrmu, hakan kuma yana faruwa ne a dalilin rashin aiki da koyarwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) ta fuskar zama na ilimi da ya yi da matansa. Uwa uba kuma shi ne, aiki da ilimin wanda kuma idan ka kale mu a yau ilimin ai akwai shi, abin da ya yi saura shi ne aiki da shi. Sa’anan kuma ya kamata mu daina karya da ha’intar junanmu. Allah Ka sanya tsoranKa a zuciyarmu, amin.”

Daga Alkhairu Ba Kula Mata, Yaba-Legas (08056109087), yana cewa: “FDK, a gaskiya ni a ganina amana da alkawari sai maza don mata mafi yawansu ’yan karya ne amma kuma akwai na kirki.”

Abbas Lawal Tela Dadin Kowa, Sabon Wuse, Tafa L.G.A Jihar Neja: “FDK, fatan alheri a gare ka. Dalilai da dama da ke sanya soyayya ta juya ta zama kiyayya, musamman ga ma’aurata bayan aure, akwai rashin tsafta, rashin ladabi da biyayya da almubazzaranhi a tsakaninsu, suna ba da gudunmowa sosai; da fatan Allah Ya ganar da mu, amin.”

Sai kuma Abdullahi Garba Kankara (07039550055): “A ganina babban abin da ke jawo soyayya ta koma kiyayya a zamanin nan na yanzu shi ne rashin gaskiya da kuma rashin yarda da juna.”

Daga Haruna Umar Hadeja (08105223000): “FDK, barka da warhaka da fatan kana cikin koshin lafiya. Ni bako ne a cikin wannan fili maei albarka. Don Allah ina so ka mika min sakon gaisuwata ga jama’ar filin nan na Dausayin Kauna, ina muku fatan alheri.”

Daga Hassan Ibrahim Warji (08121899959): “FDK, wannan batun in ka ga haka, to dama ba kauna, yaudara ce kawai, domin Hausawa sun ce so hana ganin laifi. Idan da akwai soyayya, da haka ba za ta samu ba. Na biyu kuma shi ne, kishi kumallon mata. Ka san su fa!”

Sako daga S. Tibis Legas (08071727677): “FDK, a gaskiya wannan maudi’i yana da matukar muhimmanci ga al’umma amma ni a ganina matsalar ta fi kasancewa a kan soyayyar da aka gina ta a kan karya. Idan ka lura a wannan lokaci mata sun fi son saurayi wanda zai musu karya, sai bayan an yi aure abokai sun hada wa ango kudin da zai ci da amarya taliya na wata biyu. To da zarar an ce ma kudin sun kare, za a koma cin tuwo, ita kuma za ta ce ba ta san wannan ba. To hakan na taka rawar gani wajen soyayya ta koma gaba. Allah Ka ganar da mu, amin.

Sako daga Shaibah Toro: “A gaskiya abin da ke sa soyayya ta zama kiyayaya shi ne rashin gina shi a kan tafarkin da Allah Ya shar’anta. Duk soyayyar da aka gina ta a kan tafarkin Manzo (SAW), wallahi ba ta komawa kiyayya.”

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos