Me ya sa wasu jaruman Kannywood ke talaucewa bayan sun yi tashe?

Ajiye girman kai na yi na koma tallar kunun aya don nema wa kaina mafita inji Chiroki.

Me ya sa wasu jaruman Kannywood ke talaucewa bayan sun yi tashe?

Wasu jaruman Kannywood da dama kan talauce ko su faɗa wani hali na buƙatar taimako bayan sun ɗauki dogon lokaci suna tashe a masana’antar.

To sai dai wasu jaruman masana’antar sun ce rashin tsari da tanadi daga wasu jaruman ne ke haddasa musu faɗawa ƙangin talaucin.

A tattaunawarsu da shirin Mahangar Zamani na BBC Hausa, Aminu Sheriff da aka fi sani da Momoh da kuma Bashir Bala Chiroki sun bayyana abubuwan da suke ganin su ke haddasa matsalar.

Bashir Bala Chiroki – wanda a shekarun baya ya yi tashe, a yanzu kuma yake fama da rayuwa, inda har ya koma sayar da kunun aya – ya ce abin da ke haddasa matsalar shi ne rashin tanadi da tsari mai kyau.

A ɓangaren Aminu Sheriff Momoh ya ce, yana kallon matsalar ta fuskoki uku, da farko ya ce ya danganta da yadda jarumi ya ɗauki sana’ar fim.

“Shin ya ɗauke ta ce a matsayin sana’a ko kuwa wani abu na nishaɗi da zai zo ya yi, ya kama gabansa idan an kammala?

“Abu na biyu shi ne wacce irin rayuwa ya shirya wa kansa. Ya ɗauki rayuwar ce da irin ɗaukakar da ya samu a masana’antar, ma’ana ya fita daga wani rukuni na mutane ya koma wani? Zai canja sutura da muhalli da ƙara kuɗin da yake kashewa ko kuma zai zauna a yadda yake?

“Abu na uku shi ne wane shiri ya yi wa kansa zuwa rayuwarsa ta gaba, tunda dai ita ɗaukaka zuwa take yi kuma ta tafi, shin akwai wani tanadi da ya shirya wa rayuwarsa na yadda zai ɗora bayan gushewar ɗaukakar da ya samu a masana’antar,’’ in ji Momoh.

Ya ce, waɗannan su ne abubuwan da duk wani jarumi ya kamata ya yi la’akari da su bayan shigarsa Kannywood.

Ya ci gaba da cewa, akwai jaruman da idan suna kan ganiyar ɗaukaka sai su ɗora wa kansu girman kai da ƙarya na sai sun canja matsayin da suke.

“Za ka ga mutum sai ya ce ruwa ma sai na gora zai sha, kuma ba zai ci abinci mai araha ba, sai mai tsada ko ya riƙe babbar waya ko babbar mota ko babban gida, wani ma sai ya biya kuɗi masu yawa ya kama hayar babban gida kawai saboda shi ya samu ɗaukaka’’, in ji jarumin.

‘Ajiye girman kai na yi na koma tallar kunun aya don nema wa kaina mafita’

Bashir Bala Chiroki – wanda ya gamu da irin wannan matsalar a baya, har ma ya koma sana’ar sayar da kunun aya – ya ce, a 2019 ya shiga halin matsin rayuwa.

Ya ce, shi a ganinsa matsalar shuɗewar zamani ce ta sa wasu masu shirya finafinan suka jingine shi a gefe, daga nan kuma ya ɗauki matakin nema wa kansa mafita.

“Da na ga abin ba zai yiwu ba, sai na fitar da girman kai da kunya, na je aka koya min yadda ake haɗa kunun aya, ya yi daɗi, ya yi garɗi, don rufa wa kaina asiri, na kuma riƙa ɗauka a babur ina yi masa waƙa, haka nake yi don rufa wa kaina asiri,’ in ji jarumi Chiroki.

Jarumin ya kuma ce dama kuɗin da ake biyan jarumai a fim, ba kuɗi ne da zai riƙe mutum ba, “domin ba lallai ne su riƙe ka ba, su kuma rufa maka asiri’’

Ya ci gaba da cewa, jaruman fim iri biyu ne. Akwai talakawa ko ’ya’yan talakawa; akwai kuma masu kuɗi ko ’ya’yan masu kuɗi, waɗanda ke zuwa da kuɗinsu, su kuma zuba jari domin shirya fim.

‘‘Amma su ’ya’yan talakawa da talakawan a fim ɗin suke sa ran samun abin rufin asiri, don haka idan ka faɗo cikin wannan rukuni, abin da ya kamace ka shi ne ka nemi wata

hanyar samun kuɗin, domin rufa wa kanka asiri,’’ kamar yadda Chiroki ya bayyana a cikin shirin Mahangar zamani na BBC Hausa.

‘Ba a yin dukiya da kuɗin fim’

Aminu Sheriff Momoh ya ce kuskuren da wasu jaruman masana’antar ke yi shi ne shiga harkar fim domin yin dukiya.

Ba a yin dukiya da kuɗin fim, duk wanda zai sa a ransa cewa zai yi dukiya da abin da za a biya shi a fim, to, ya yi kuskure’’, in ji Momoh.

Ya ƙara da cewa, arzikin da mutum zai samu a fim bai ya wuce masoya waɗanda ke kallon jarumi kuma yake burge su, su kuma suke son sa ba, amma ba kuɗin da ake biya a masana’antar ba.

Ya ce, babban abin da ya kamata kowane jarumi ya yi shi ne ya nema wa kansa wata sana’a ko aikin da zai dogara da kansa, koda ba a neme shi harkar fim ba, to yana da sana’ar da zai dogara da kansa don ya sama wa kansa mafita.

“Idan za ka zauna tsawon wata guda ba a gayyace ka fim ba, kuma kana da iyali, to, me za ka ciyar da su?,’’ in ji shi.

Momoh ya ce, sauran ma’aikatan Kannywood waɗanda ba sa fitowa a matsayin jarumai, sun ma fi jaruman dama, saboda su suna da damar yin aiki a wasu kamfanoni ko ma’aikatu, saɓanin su jaruman waɗanda kawai fitowa suke yi a matsayin taurarin fim.

‘Wani lokaci kuɗin da ake biyan jarumai ko na mota ba ya isa’

Bashir Bala Chiroki ya ce abin da ake biya a fim ya bambanta daga furodusa zuwa furodusa, domin a cewarsa wani furodusan zai biya isassun kuɗi saɓanin wani.

Ya ce, ‘‘A wani lokacin idan na yi fim akan biya ni Naira 10,000 ko 20,000 ko 30,000; wani lokacin kuma Naira 5,000 ko ma 3,000. Shi fim ba babba ba ƙarami ya danganta da wane ne ya ɗauke ka’.’

“Wani idan ya biya ka kuɗin fim, wallahi sai ka yi wata shida kana kashewa, amma wani idan ya biya ka wallahi idan ka sake kuɗin motar komawa gidanka ma sai ka yi rance.

Saboda harkar fim akwai riba; akwai faɗuwa. Wani idan ka gama yi masa fim, sai ya ce maka wane ma haɗu’’, in ji jarumin.

Chiroki ya ce, yana da kyau a ƙara kuɗin da ake biyan taurarin finafinan Kannywood, kodayake a cewarsa yanzu an ɗan samu sauyi, wasu sun fara ƙara kuɗin da suke biyan jarumai.