Me ya sa ’yan Najeriya ke debe tsammani kan Super Eagles?

Shin ko dai Najeriya ta yi zabin tumun dare wajen dauko Peseiro?

Me ya sa ’yan Najeriya ke debe tsammani kan Super Eagles?

A ranar Juma’ar da ta gabata, baya ga zafin gari saboda yanayin rashin kudi a hannu, ga kuma zafin yunwa ga wadanda suke Azumin Ramadan, kwatsam sai ga wani zafin – an biyo tawagar Super Eagles ta Najeriya har Abuja – an mata ci daya mai ban haushi.

Kash! Zafi uku ke nan ga wasu, wasu kuma zafi biyu.

“Ni dai babu ruwana. Duk wanda ya ga zai iya shi ya sani. Ni dai babu ruwana da goyon bayan tawagar Super Eagles,” inji Sani Scorer, wani dan kwallo, wanda ya dade yana kallon Super Eagles, amma ya ce ya fid-da tsammani da tawagar.

A cewarsa, “Super Eagles ba za ta taba canjawa ba. Na fi shekara 40 ina goyon bayan tawagar, amma na gaji. Ba za su saka min ciwon zuciya ba. Ai ba ibada ba ne.”

Ya kara da cewa, “Cin hanci da rashawa da kabilanci ya shiga tawagar. Ba a saka Hausawa da yawa duk da sun iya kwallo.”

A ranar, kasar Guinea-Bissau ce ta ci daya mai ban haushi a wasan neman gurbin shiga Gasar Nahiyar Afirka ta 2024.

Kasar ta Guinea-Bissau ba ta taba doke Najeriya ba, wanda hakan magoya bayan Najeriya suka je kallon wasan hankalinsu a kwance da tunanin nasara tasu ce.

An fara wasan ne Najeriya na saman teburi da maki shida, bayan ta doke Saliyo da Sao Tome and Principle, sannan Guinea-Bissau ke biye mata da maki hudu.

Yanzu dai Najeriya ta koma ta biyu da maki shida, Guinea-Bissau na da maki bakwai.

A gaban tawagar Super Eagles, dan wasan Napoli, Victor Osimhen wanda shi ne yake kan gaba wajen zura kwallo a Gasar Seria A a yanzu, da dan wasan Atlanta na Italiya, Ademola Looqman da Chukwueze ne.

Wannan ya sa hankalin magoya bayan Najeriya suka samu sakina, amma wasu kuma suke cewa duk zaratan ‘yan wasan da Najeriya ta tara, hankalinsu ba zai kwanta ba, domin a cewarsu, Najeriya ba ’yan goyo ba ne.

A zagaye na farko na wasan ne Mama Balde ya zura kwallo daya a ragar Najeriya, abu kamar wasa kwallon daya ta makale har aka tashi.

Haka aka tashi, wasu na murna suna yi wa magoya bayan tawagar dariya, wasu kuma suna bakin ciki.

Da yake jawabi bayan wasan, Kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya ce, “Ina tunanin mun nuna kwarewa matuka a minti 30 na farko, amma ba mu samu nasarar zura kwallo ba.

Ya bayyana karara cewa sun fi Guinea-Bissau iya kwallo. “Wani lokacin tawagar da ta fi iya kwallo tana rashin nasara.”

Sai dai mai horarwar, wanda dan asalin kasar Portugal ne, ya ce yana da yakinin Super Eagles za ta lallasa Guinea-Bissau da akalla ci uku da nema a wasa na biyu.

Ko dai Najeriya ta yi zabin tumin dare wajen dauko Peseiro?

A watan Mayun bara ne Hukumar Kwallon Kafar Najeriya, NFF ta dauko Jose Peseiro domin ya maye gurbin kocin wucin gadi, Augustine Eguavoen, wanda ya jagoranci tawagar ta Super Eagles zuwa Gasar Nahiyar Afirka, inda aka yi waje da Najeriya a wasan farko na zagaye na biyu.

A karkashin kulawar Peseiro, Najeriya ta samu nasara a wasa biyu; Saliyo da Sao Tome and Principle.

Sai dai kasar ta sha kaye a wasa biyar; Mexico da Ecuador da Aljeriya da Costa Rica da Portugal.

Jose Santos Peseiro tsohon dan kwallo ne mai shekara 61 da ya buga tamaula a matsayin dan wasan gaba.

Ya taba horar da kungiyoyin Sporting CP ta Portugal da FC Porto da Real Madrid a matsayin mataimakin koci, da tawagar kwallon kafa ta Saudiyya, sannan a karshe-karshe ya horar da kasar Venezuela, inda suka rabu a watan Agustan shekarar 2021.

Kociyan AS Roma, Jose Mourinho ne ya ba Hukumar NFF din shawarar ta dauki Peseiro a matsayin mai horar da ‘yan wasanta.

Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa kocin bai nuna bajinta a tsofaffin kungiyoyi da tawagar kasashen da ya horar ba.

Sai dai a duk sanarwar da aka yi game da kocin, cewa kawai ake yi kwararre ne, ba a taba fada cewa kasashe da yawa sun kore shi ba.

Misali, a zamaninsu a shekarar 2014 shi da mai gidansa, Carlos Queiroz, Real Madrid ta sallame su saboda tabarbarewar da kungiyar ta yi, sannan shi Queiroz din ya ce ba zai iya doke Barcelona a kakar ba.

A shekarar 2007 kuma kocin ya ajiye aiki a Kungiyar Panathinaikos saboda ya gaza gyara kungiyar. Sannan a shekarar 2008, Kungiyar Rapid Bucuresti ta Romania ta sallame shi.

A shekarar 2001 kuma kasar Saudiyya ta sallame shi, sannan Kungiyar FC Braga ma ta sallame shi a shekarar 2016.

Haka kuma, Kungiyar Sharjah da ke Dubai ta sallame shi a shekarar 2017 bayan wata tara kacal, sannan ya koma Sporting Braga, amma nan ma aka kore shi a shekarar.

A shekarar 2020 ya koma tawagar Venezuela, amma aka rika lallasa tawagar, wanda hakan ya sa kasar ta sallame shi a shekarar 2021, duk da cewa ya ce matsalar rashin biyan albashi ne ya janyo rabuwar.

Duba da shekarun da ya yi yana horar da ‘yan wasa ya nuna cewa ba ya dadewa a waje daya. Sau daya ya taba zama a Kungiyar Clube Oriental de Lisboa, inda ya shekara hudu.

Shin zai iya gyara Super Eagles?

Bincike ya nuna a shekarun da ya yi yana horar da ‘yan wasa, babu wani kofin ko wata gasa da ya tabe lashewa.

Sai dai ta yiwu akwai rashin zaratan ’yan wasa a wuraren da ya horar.

Amma Najeriya na da zaratan ‘yan wasa matasa da duniya take ji yanzu.

“Ba na tunanin zai iya yin wani abu. Najeriya ta fi bukatar koci dan Najeriya wanda ya san yanayin kasar saboda muna son wanda zai iya hada kan kasar,” inji Abubakar Abdullahi, wani mai bibiyar tawagar Super Eagles.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa