Me ya yi wa batun auren Sani Rainbow da Rahama Hassan kafar ungulu?
Yau kimanin shekara guda ke nan da ake jiran ranar daura auren fitaccen dan kasuwar fina-finan Hausa Sani Rainbow da kuma jaruma Rahama Hassan, inda har aka rika yada jita-jitar an daura auren cikin sirri, inda daga baya aka samu tabbacin ba a daura auren ba.A yanzu haka batun auren Rainbow da kuma Rahama yana-kasa-yana-dabo, […]


Yau kimanin shekara guda ke nan da ake jiran ranar daura auren fitaccen dan kasuwar fina-finan Hausa Sani Rainbow da kuma jaruma Rahama Hassan, inda har aka rika yada jita-jitar an daura auren cikin sirri, inda daga baya aka samu tabbacin ba a daura auren ba.
A yanzu haka batun auren Rainbow da kuma Rahama yana-kasa-yana-dabo, domin babu wani takaimaiman batu a kansa.
A wata hira da jaruma Rahama ta yi da Mujallar Fim a watan jiya ta bayyana cewa batun aurensu na nan daram, inda har ta ce lokaci kawai suke jira, bugu da kari ita da Sani akwai soyayya mai karfi ta kamar za su hadiye junansu.
A yayin hirar ta ce: “Ina nan a kan maganar auren, sai na ga abin da ya ture wa buzu nadi. Maganar aure ta nan lokacin Allah ne kawai bai yi ba.”
Ta ce zancen an daura aure karya ne, amma Rainbow masoyinta ne, kuma shi take kudurin aure.
Da aka tambaye ta ko me ya jawo har yanzu ba a daura musu aure ba kasancewar ta daina fim fiye da shekara daya don batun aure, anya a cikinsu babu mai yi wa dan uwansa yawo da hankali sai ta ce, “Babu. Muna son junanmu sosai, akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninmu.”
Wata majiya da ke kusa da Rainbow ta bayyana wa wakilinmu cewa ’yan uwansa ne ba sa sonta.
“Abin da yake faruwa shi ne, mahassada sun shiga gidansu Sani, inda suka rika yin miyagun maganganu a kan jarumar, wasu sun ce ma ai ta fi shi wayo, tun da ’yar boko ce, don haka ba zai iya ba ta umarni ta bi ba. Wannan al’amari ya yi tasiri a gidansu Rainbow.” Inji majiyar.
Wata majiya kuma ta ce, “Rainbow yana da mata biyu kuma kowacce gidanta daban, uwargidan ce take ta bala’i don ganin ba a yi auren ba, bugu da kari ta samu daurin gindi a wurin ’yan uwan mijinta.”
“Rahama tana son Rainbow kamar za ta hadiye shi, don shi ta daina fim yau shekara daya ke nan, mafarkinta a daura masa aure da shi. Ta fada mini inda ta rantse cewa za ta bi umarninsa, ko kara ya ajiye ba za ta tsallake ba. Allah Ya jarabce ta da sonsa, babu wani abu da ta sa a gaba face aure.” Inji wata majiya.
Wakilinmu ya tura wa Rainbow sako mai dauke da tambayoyi kamar haka: Tun bayan da Rahama Hassan ta yi hira da Mujallar Fim ne zance ya cika gari cewa an daura muku aure cikin sirri, me za ka ce kan hakan? Shin akwai batun auren? Idan akwai an sa rana? Ina batun cewa ’yan uwanka ne suka hana ka aurenta? Daga nan sai Wakilinmu ya buga masa waya ganin bai turo amsoshin tambayoyin ba, daga farko ya dauka, sai dai bayan Wakilinmu ya kara gabatar masa da tambayoyin ne sai ya kashe wayarsa, a nan Wakilinmu ya ci gaba da kiransa, amma ya ki daga wayar, sannan bai kuma ba da amsoshin tambayoyin ta hanyar turo da sako ba.
Bayan nan Wakilinmu ya kara tuntubar jarumar don hakikanin wurin da aka tsaya kan batun aurenta da Rainbow sai ta ce a yanzu dai ba ta da wani abu da za ta ce bayan wanda ta fada a Mujallar Fim, har yanzu tana kaunarsa.
“Babu wani abu da zance, idan ma ya fadi wani abu, to ni dai har yanzu ina kan bakata a kan maganar aurenmu.” Inji Rahama.
Yanzu abin tambaya a nan shi ne, me ya yi wa batun auren Rahama Hassan da Sani Rainbow kafar ungulu?