Me zai faru idan masu dauke da rabin Sikila suka yi aure?

Wace shawara za ka bai wa wadanda suka yi aure ba su yi gwaji ba alhalin dukkansu suna da rabin ciwon Sikila, wato su a zahiri lafiyayyu ne? Daga Shehu M.K Amsa: A’a to wace shawara kuwa? Za a raba aure ne domin ana tsoron haihuwar Sikila? A Turai dai yadda ake yi shi ne […]

Me zai faru idan masu dauke da rabin Sikila suka yi aure?

Wace shawara za ka bai wa wadanda suka yi aure ba su yi gwaji ba alhalin dukkansu suna da rabin ciwon Sikila, wato su a zahiri lafiyayyu ne?

Daga Shehu M.K

Amsa: A’a to wace shawara kuwa? Za a raba aure ne domin ana tsoron haihuwar Sikila? A Turai dai yadda ake yi shi ne idan matar ta samu ciki a rika auna cikin tun kan a haifo shi a gani idan Sikila ne a zubar da shi, idan ba Sikila ba ne a kyale shi. Akwai gwaji iri biyu. Su haka suke yi. Amma a irin al’adarmu da addininmu ba za a ce a yi haka ba a yanzu. Sai dai fa idan malamai ne za su hadu su yi fatawa a kan haka tunda lokacin da ake wannan awon a mako na 10 ne zuwa 16, bai kai lokacin da ake hura wa jariri rai ba. Idan kuma akwai wani malami da ka sani da ya ba da fatawar za a iya yi to.

A lissafin kimiyya kashi 25 cikin 100 na abin da za su haifa ne za su samu ciwon Sikila, idan ma an haifo din ke nan. Idan aka ce kashi 25 mutum sai ya dauka a cikin ’ya’ya hudu za a samu daya ke nan. A’a shi yadda wannan lissafin yake shi ne babu wanda ya san wannan kashi 25 cikin 100 din su ne za su zo a farko ko a tsakiya ko a karshe, ko a tare, ko daban-daban, sai fa wanda Ya yi su. Domin na san wadanda suke da rabin ciwon masu yara tara amma na tara ne kadai mai ciwon, daga nan suka daina haihuwa. Ka ga ke nan nasu a karshe suka zo. A daya hannun kuma akwai wadansu iyayen dukkansu masu rabin ciwon amma masu Sikila sun fi yawa a cikin ’ya’yansu. Ka ga wadannan a iya cewa a cakude suka zo da masu lafiya. Akwai ma masu rabin ciwon da duka ’ya’yansu Sikila ne. Wato dai don haka sai dai addu’a.

Ina so a mini karin haske ne a kan ajin jini. Shi mai ajin ’O’ an ce ba ya da antigen. Wannan na nufin ba zai kamu da cututtuka sosai ba ko kuwa? Su kuma masu ‘AB’ an ce ba su da antibody. Wannan na nufin ba su da kariya ke nan?

Daga A. Danfuloti

Amsa: A’a antibody da antigen da ake magana a nan na kwayoyin jini ne ba na cututtuka ba. Domin akwai antibody iri biyar, IgA, IgD, IgE, IgG da IgM. Akwai na kan jajayen kwayoyin jinin da kake magana, su ne IgM, akwai uku na kariya daga cututtuka su ne IgA, da IgG da IgD, akwai kuma masu sa borin jini su ne IgE.

Ina yawan haki ba tare da na yi wani aiki ba. Ko shin matsala ce?

Daga Hafsa Muhammad, Kano

Amsa: Eh, matsala ce, alamu ne na cewa akwai matsala watakila ta karancin jini ko ciwon zuciya ko hawan jini ko na hanta ko na koda da sauransu. Mai samun irin wannan alamu sai ya je asibiti an binciki mene ne dalili.

Yawan shan citta yana da illa ne ga lafiya? Domin ni kusan kullum sai na sha shayi mai citta

Daga Musa U.

Amsa: A’a ba wata matsala.

Me ke kawowa cikin barci miyau ya rika yawa a bakin mutum ya rika dalala, ko ma ya wuce kamar ya sarke mutum?

Daga Nasir Nobiso

Amsa: Bambancin halitta ne ba ciwo ba ne. Wadansu mutanen idan suna barci da miyau ya taru suke hadiyewa ba su ma sani ba, wadansu kuma sai dai ya dalalo. Akwai ma wasu abubuwa kamar amfani da wasu magunguna ko samun juna biyu sukan iya jawo haka.

Idan na ci abinci nakan wanke bakina amma bayan haka sai bakina ya yi tsami-tsami tamkar na kwana ban wanke ba. Shin me ke kawo wannan?

Daga El-Ishak Maiyaki, Kano

Amsa: Ka samu ka je likitan hakori ya wanke maka su sosai, ya kuma gaya maka da me da me ya kamata ka rika wanke hakoran.

Ka ce maganin gargajiya mai daci yana da illa. To na asibiti masu daci fa? Su basu da illa?

Daga Hassan Ibrahim Warji

Amsa: A’a su ai magungunan asibiti sai an tace an auna dacin da ma kowace guba idan akwai, an tabbatar ba za su illa ga jiki sosai ba. Da ma maganar tacewa da aunawa ake, aka ce su masu gargajiya ba mu sani ba ko suna tantance sinadaran amfanin da ke cikin sassaken daga sinadaran da ba masu amfani ba, kamar daci da guba, kuma ko suna tace dacin da gubar ko a’a.

Duk lokacin da zan sha kunu ko fura sai na sa sukari amma likita ya hana ni. Ko me zan sa a madadin sukarin?

Daga Malam Ashiru, Katsina

Amsa: Duk abin da za ka sa mai zaki a abin sha sukari ne dai tun daga zuma ko ruwan siraf ko lemon zaki da sauransu. Yana da kyau a san dalilin da aka hana ka shan sukarin, yawanci dai ciwon Suga ne. To in dai ta kama sai ka sa sukari kake iya shan abubuwa, za ka iya sa kadan, kamar karamin cokali daya kacal na sukarin ko na zumar ko na lemon zakin kamar yadda yawancin mutane masu son su zauna lafiya suke yi. Wadansu za su iya cewa ka sha sikarin, tunda shi zakinsa ba ya shiga jini. Amma amfani da sukari kadan din ya fi na sikarin. Ba wanda zai hana mai ciwon suga shan sukari kwata-kwata, in dai yana shan magani yadda ya kamata, sai dai a ce ya sha dan kadan. Masu ciwon suga da ba sa shan sukari dan kadan a rana ma za su iya samun matsalar suma ta saukar sukari wato hypoglycaemia.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50