Mene ne laifin Manjo Hamza Al-Mustapha?

Mabambantan ra’ayoyi na ta yawo kan Manjo Hamza al-Mustapha, tun bayan da kuliya ya wanke shi daga laifin da ake zarginsa akan kisa zargin babban dogarin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha a cikin harkokin siyasa da kuma rashin komawarsa a gidan soji. A kan wannan wasu da dama ke bayyana cewar wai domin ya […]

Mene ne laifin Manjo Hamza Al-Mustapha?
Mene ne laifin Manjo Hamza Al-Mustapha?

Mabambantan ra’ayoyi na ta yawo kan Manjo Hamza al-Mustapha, tun bayan da kuliya ya wanke shi daga laifin da ake zarginsa akan kisa zargin babban dogarin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha a cikin harkokin siyasa da kuma rashin komawarsa a gidan soji. A kan wannan wasu da dama ke bayyana cewar wai domin ya taimaka wa Shugaba Jonathan ne dalilin da ya sa kotu ta sallame shi, duk kuwa da cewar gaskiyar lamari shi ne bayan kwakkwaran binciken kotu ta tabbatar da cewar ba ya da hannu a abin da ake zarginsa a kai.
A yayin da wannan ke faruwa, sai kwatsam aka ji Manjo Almustapha ya mayar wa da tsohon Shugaban kasa Olusegun  Aremu Mathiew Obasanjo martani akan zazzafar wasika irin  ta farko da tsohon shugaban ya rubuta wa Jonathan, wadda a ciki ya bayyana tsohon dogarin a matsayin wanda Gwamnatin Tarayya ta hada hannu da shi wajen horas da matasa ‘yan sari-ka-noke wadanda za su dauki rayukan abokan hamayya dubu daya gabanin zaben 2015.
Abu mai muhimmanci shi ne mayar da martanin da Manjo Almustapha ya yi duk kuwa da cewar Obasanjo bai fito karara ya ambaci sunansa ba, sai dai a fakaice, wanda a kan wannan nake ganin dacewar kiran da tsohon jami’in sojin ya yi wa Obasanjo kan ya fito a yi mukabalar ga-wuta-ga-masara kan lamurran da suka shafi kasa, gabanin ya zama shugaban Nijeriya zuwa yau.
Kamar dai yadda muka sani duk da cewar Manjo Almustapha kakkarfa ne, kuma nagartaccen jami’in soji ne wanda ba ya da tsoro ballantana shakku, wanda akan hakan ne ya fito fili ya wanke kansa, tare da ranstuwa da UbangijinSa kan rashin sahihancin kalaman Obasanjo. Bugu da kari ko da bai fada ba, mun san bai taba ba, kuma ba zai taba sa kansa a lamari irin wannan ba.
Yana da kyau jama’a mu yi duba, tare da nazarin zalunci, azabtarwa da kiyayyar da wasu daga cikin shugabanni suka nuna wa wannan bawan Allah, ba tare da hakkinsa ba, a tsayin shekarun da ya kwashe a gidan maza. A haka duk da Ubangiji ya dube shi da idon rahama ya fitar da shi, amma kuma suna biye da shi tare da shirya masa kulle-kulle da makirce-makircen ganin baya a kokarinsu na shafa masa bakin fenti, domin Arewa da ‘yan Arewa da ma al’ummar kasa su dawo daga rakiyarsa, wanda akan wannan muke cewa ta Allah ba ta su ba, ba za su taba ganin abin da suke so ba.
Na fadi hakan ne, domin duk wani mai hankali da tunani ya san irin tuggu da manakisar da Obasanjo da sauran makiyan Arewa suka yi wajen ganin Almustapha ya karasa rayuwarsa a gidan kurkuku da kuma yadda a yau suke bakin cikin irin gagarumar karbuwa da jajantawar da ya samu ga al’ummar ciki da wajen kasar nan baki daya.
Ko ba a fada ba, tabbas Manjo Almustapha masoyin Arewa ne da Najeriya baki daya ta yadda yake taimakon yankin da al’ummar yankin, kamar yadda ya fada a wata hira da aka yi da shi, inda ya ce tun a shekarar 1984 yake tafiyar da abubuwa da dama na taimakon matasa ta fuskar nemar masu ayyukan yi da tallafa masu a karatu da sana’o’i domin su zamo masu dogaro da kansu.
A cewarsa, Arewa na bukatarsa da neman taimakonsa don haka a matsayinsa na dan Arewa mai kishin Arewa da son ci-gabanta zai ci-gaba da iyakar kokarinsa, domin ganin ya taimaki al’ummar yankin ta fuskoki da dama.
Shin wai me ya sa ake son ganin bayan mai wannan tunani da hangen nesan? A bayyane mun san saboda tsayuwarsa akan gaskiya da kokarin ganin an kawar da shi; a can baya mun ga yadda aka dauki hayar wadanda suka shiga kotu domin gabatar da shaidar karya akan karya, amma kuma daga baya suka yi nadama, suka kuma fito fili suka bayyana wa duniya. Bayan wannan ya wuce a yanzu sabon salon tozarta wannan bawan Allah da aka fito da shi, shi ne ta hanyar daukar hayar Malamai masu wa’azi wadanda ke da rauni, domin su rika yada batanci kansa.
A daya gefen baya ga wasu rubuce-rubucen aibantawa da ake yi a kansa, wanda muke fatar jama’a da su hankalta, su kuma sani cewar makiyan Arewa ne ke dauke da alhakin hakan.
Yana da kyau al’ummar Arewa ka da mu bari hankalinmu ya fita daga kanmu, da har za mu danne gaskiya akan karya da kuma yadda da kalaman manyan makiyan Arewa a kan masoyan Arewa na hakika.
Daga karshe nake son mu kara lura da cewar Manjo Almustapha ba ya da kowane irin laifi da ya yi wa al’ummar Arewa da kasa baki daya, da har za a ki shi, ko a guje shi, ko a yi kokarin bata masa suna. Abin da muka sani shi ne masoyinmu ne, wanda ke kaunar ci-gabanmu. Hasali ma akan wannan ne muke fatar Ubangiji ya ci-gaba da kariyarsa daga duk wani makirci da kullalliyar da ake yi a kansa.
M A Farouk Sokoto Mai sharhi ne a kan al’amurran yau da kullum. Ya rubuto daga Sakkwato.
07014414414

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno