Mercy Johnson ta jingine shirin fim

Mercy Johnson, shahararriyar ’yar wasan fim a Kudancin Najeriya ta kuduri aniyar jingine shirin fim saboda karatowar haihuwa, ganin yadda cikinta ya fara tasawa.’Yar fim din, wacce take da dimbin masoya, ta tabbatar wa manema labarai cewa lallai ta jingine harkar fim har sai ta haihu, ta murmure sannan ta dawo ruwa.Mercy, wacce a bana […]

Mercy Johnson ta jingine shirin fim
Mercy Johnson ta jingine shirin fim

Yar fim, Mercy-JohnsonMercy Johnson, shahararriyar ’yar wasan fim a Kudancin Najeriya ta kuduri aniyar jingine shirin fim saboda karatowar haihuwa, ganin yadda cikinta ya fara tasawa.
’Yar fim din, wacce take da dimbin masoya, ta tabbatar wa manema labarai cewa lallai ta jingine harkar fim har sai ta haihu, ta murmure sannan ta dawo ruwa.
Mercy, wacce a bana ta cika shekara 29 a duniya, ta yi aure ne a watan Agusta na 2011, inda wannan shi ne karo na biyu da za ta haihu. An samu labarin cewa tana zaune ne cikin jin dadi tare da mijinta, Prince Odianosen a Legas, garin da dama aka haife ta.
Ba wannan ne karo na farkoda ’yar wasan ta taba jingine harkar fim ba, domin kuwa a 2012 ma, lokacin da ta haifi diyarta ta farko mai suna Purity, ta jingine harkar fim, sai daga bisani, bayan ta murmure ta dawo ruwa. A wannan karon ana zaton ’yar wasan ba za ta dade ba za ta dawo fim, domin kuwa akwai aiki da yawa da ke jiranta.