Mesa: Ga ban sha’awa, ga hatsari
Duk girman mesa ba ta da dafi, in ji masana.
Idan ana batun kyau da hatsari, ba a baro mesa a baya ba, saboda ta siffatu da wadannan abubuwa biyu.
Mesa na daga cikin dangin macizai da ake ganinsu a gida da daji a sassan duniya.
- Sarkin dawa: Dabbar da ake jin gurnaninta daga nisan mil 5
- Rayuwar dabbobi: A ina kunnuwan fara suke?
Maciji ne wanda masana suka ce ya fara bayyana a yankunan Asiya da Afirka, kana daga bisani ya bazu a duniya.
Sabanin sauran macizai, masana sun ce duk girman mesa ba ta da dafi, kuma tana da ban-sha’awa.
Kwaro ne wadda ake iya ganin shi a ko’ina a wannan zamani, walau a gidajen daidaikun jama’a ko gidajen adana dabbobi.
Wasu mutane kan ajiye mesa a gida saboda sha’awa da makamancin haka.
Bari mu dubi wasu siffofi da mesa ta kebanta da su domin kyawun fahimta:
Duk girman mesa ba ta da dafi. Takan yi amfani da karfin da Allah Ya yi mata ne wajen farautar manyan dabbobin da take ci, hatta mutum ba ta kyalewa idan ta samu.
Da farko takan cafke abin farautarta da baki sannan ta yi maza ta kanannade shi jikinta ta yi mika.
Ta haka take takura wa abin da ta kama ya kasa numfasawa da hana jini gudana a jikinsa yadda ya kamata, ta kuma kakkarya shi don samun saukin hadiya.
Tana iya hadiye abin da ta kama duk girmansa. Misali, a 2017 an kama wata mesa da aka gano ta hadiye gawar wani mutum a kasar Indonesiya.
Da zarar kwan da ta zuba suka kyankyashe, babu ruwanta da ’ya’yan sai dai kowa ya yi ta kansa. Wanda ya rayu, ya rayu, wanda kuma ya mutu ko kwari suka cinye shi, shi ke nan.
Mesa ba ta dara-daran hakora balle ta tauna abinci, wannan ya sa duk abin da ta kama sai dai hadiya kawai.
Daga cikin bakinta ya gangara zuwa ciki kamar roba ce, tana ina budewa da kuma tsukewa. Wannan ya sa take iya hadiye abu duk girmansa.
Mesa da sauran macizai na da baiwar iya wangame baki fiye da girman jikinsu.
Mesa na iya rayuwa har shekara 40 ko sama da haka idan ta samu kulawa ta musamman. Amma saboda irin kalubalan da suke fuskanta musamman daga bangare masu farautar macizai, da wuya a samu mesar da ta haura shekara 20 a wannan zamani.
Tsayin rikakkiyar mesa na kai kafa 25 ko fiye da haka.
Kyawun launi da kwalliyar da ke jikin fatarta ya sa akan yi amfani da fatar wajen sarrafa abubuwan amfani kamar jaka da takalmi da sauransu.
A wanna zamani ana gonar mesa inda akan kiwata su nau’ika daban-daban don amfanin mabukata.