Messi ya kafa sabon tarihi a FC Barcelona

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din FC Barcelona na Sifen sun ce shahararren dan kwallon kulob din, Lionel Messi ya kafa sabon tarihi a kulob din a ranar Asabar da ta wuce bayan ya lashe Kofin La-Liga har sau takwas. Kulob din Barcelona ya lashe Kofin La-Liga sau 8 a tsakanin shekara 11. Hakan […]

Messi ya kafa sabon tarihi a FC Barcelona

Lionel Messi

Rahotanni da ke fitowa daga kulob din FC Barcelona na Sifen sun ce shahararren dan kwallon kulob din, Lionel Messi ya kafa sabon tarihi a kulob din a ranar Asabar da ta wuce bayan ya lashe Kofin La-Liga har sau takwas.

Kulob din Barcelona ya lashe Kofin La-Liga sau 8 a tsakanin shekara 11.

Hakan ya sa Messi ya lashe wannan gasa fiye da kowane dan kwallo a FC Barcelona kawo yanzu.

Hatta Andre Iniesta, tsohon dan kwallon kulob din bai kama kafar Messi a yawan lashe kofin La-Liga ba.

Messi ne ya zura kwallo daya tilo a ragar Lebante a ranar Asabar da ta wuce bayan ya canja Philip Coutinho jim kadan da komawa hutun rabin lokaci da hakan ya sa aka tashi wasan ci 1-0.  Wannan nasara ce ta ba FC Barcelona damar lashe gasar ta bana duk da ana saura wasanni biyu a kammala gasar.