Messi ya koka kan yadda aka yi masa binciken kwa-kwaf

Shahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen kuma haifaffen Ajantina Lionel Messi ya koka a kan yadda Hukumar shirya kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta yi masa binciken kwa-kwaf na gwajin yiwuwar amfani da kwayoyi kafin wasansu da kulob din PSG da ke Faransa a ranar Larabar da ta wuce.’Yan wasa biyar ne […]

Messi ya koka kan yadda aka yi masa binciken kwa-kwaf
Messi ya koka kan yadda aka yi masa binciken kwa-kwaf

Shahararren dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen kuma haifaffen Ajantina Lionel Messi ya koka a kan yadda Hukumar shirya kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta yi masa binciken kwa-kwaf na gwajin yiwuwar amfani da kwayoyi kafin wasansu da kulob din PSG da ke Faransa a ranar Larabar da ta wuce.
’Yan wasa biyar ne dai Hukumar ta zabo daga kulob din na FC Barcelona don yi musu gwajin yiwuwar amfani da kwaya kafin wasan da suka hada da Lionel Messi da Andre Ineista da Iban Rakitic da Claudio Brabo da kuma Jordi Alba.
Sai dai daga cikin wadannan ’yan kwallo da aka zakulo Lionel Messi ne kadai aka yi masa binciken da ya zarce na kowa kuma hakan ce ta sa ya koka a kan yiwuwar ko akwai wata manufa ce ta daban ce a kansa.
Jim kadan da gama gwajin ne dan kwallon ya bayyana bacin ransa a kafar sadarwarsa ta Instagram inda ya koka a kan binciken kwa-kaf din da aka yi masa musamman a wannan lokaci da yake takarar Gwarzon dan kwallon Duniya.