Messi ya sake kafa sabon tarihi a Gasar Kofin Duniya
Messi ya cimma wannan bajinta ne bayan da ya ci ƙwallo a wasan ƙarshe na rukuni da ƙasarsa ta doke Jordan da ci 3-1.
Fitaccen ɗan wasan tawagar Argentina, Lionel Messi, ya sake kafa wani sabon tarihi a Gasar Kofin Duniya, bayan da ya zama ɗan wasa na farko a tarihin gasar da ya zura ƙwallo a wasanni bakwai a jere.
Messi ya cimma wannan bajinta ne bayan da ya ci ƙwallo a wasan ƙarshe na rukunin J da ƙasarsa ta doke Jordan da ci 3-1.
- An yi zaɓen ƙananan hukumomi lafiya a Gombe — Gwamna Inuwa
- Zaɓe: APC ta lashe kujerun ciyamomi da kansiloli a Gombe
Ko da yake ba a fara wasan da Messi ba, sai bayan kusan minti 60 da fara wasan ya shiga.
Amma duk da haka, Messi ya nuna ƙwarewarsa ta hanyar zura ƙwallo a bugun tazara a minti na 80, lamarin da ya tabbatar masa da wannan sabon tarihi a duniyar ƙwallon ƙafa.
Kazalika, Messi ya ci gaba da jan zarensa a matsayin ɗan wasan da ya fi zura ƙwallo a tarihin gasar, inda a yanzu ya jefa 19 jimilla.