Messi ya sake lashe kambun Ballon d’Or a karo na 8

Ya lashe ne bayan ya jagoranci ƙasar shi wajen lashe kofin duniya a bara

Messi ya sake lashe kambun Ballon d’Or a karo na 8

Lionel Messi ya sake lashe kambun gwarzon dan kwallon kafa na duniya wato Ballon d’Or a karo na 8 a wani kasaitaccen biki da aka yi a birnin Paris na Faransa, ranar Litinin.

Mai shekara 36, Messi ya karbi kambun ne a bana daga hannun Karim Benzema, saboda irin rawar da ya taka a kakar wasa ta bara, musamman yadda ya jagoranci ƙasar shi ta Argentina ta lashe kofin duniya da aka yi a kasar Qatar.

Erling Haaland ne dai ya zo na biyu bayan an kammala kidaya kuri’u, yayin da Kylian Mbappe ya zo na uku, Kevin De Bruyne kuma na hudu.

Tsohon dan wasan na Barcelona, Messi, dai ya zura wa Argentina kwallo har sau bakwai a gasar, kuma shi aka naɗa gwarzon gasar bayan kasar shi ta lallasa Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan karshe.

Dan wasan ya fara lashe kambun Ballon d’Or ɗinsa na farko ne a shekara ta 2009.

Shi ma dan wasan PSG, Mbappe, tauraruwarsa ta haska a gasar ne saboda ya fitar da kasar shi kunya inda ya kare da kambun wanda ya fi kowa yawan zura kwallaye a cikinta.

Mbappe dai ya zura kwallaye takwas ne a gasar, inda ko a wasan karshe sai da ya ci kwallaye uku rigis, wato hat-trick a Turance.