Messi ya zura kwallo ta 800 a tarihinsa na sana’ar tamaula

A yanzu ya ci wa Argentina kwallaye 98 a tarihi.

Messi ya zura kwallo ta 800 a tarihinsa na sana’ar tamaula

Lionel Messi ya zura kwallo ta 800 a tarihi tun daga farkon fara sana’arsa ta murza leda zuwa yanzu.

Messi ya jefa kwallon ce a wasan sada zumuntar da ya gudana tsakanin Argentina da Panama jiya Alhamis wanda aka tashi 2 da nema a birnin Buenos Aires.

Messi mai shekaru 35 da ya lashe kyautar Ballon d’Or 7 ya zura kwallon ne a bugun tazarar da Argentina ta samu gab da karkare wasa bayan kwallon da matashi Thiago Almada ya zura tun a mintuna farko na wasan.

Bayan da kwallon ta fada cikin koma, anga yadda gabakidaya filin wasan ya dau sowa yayinda aka rika wasa da tartsatsin wuta wadanda ke fitar da sunan Messi a jiki.

Akalla mutane miliyan 1 da rabi ne suka nemi shiga filin wasan mai daukar mutum dubu 83 amma kuma hukumomi suka dakile su wanda ya tilasta musu kallon wasan a akwatunan haska wasa na kan tituna.

Kawo yanzu dai Messi ya ci wa Argentina kwallaye 98, kuma shi ne na uku a jan ragamar ’yan wasa mafi jefa wa kasarsu kwallo a tarihi.