‘Messi zai yi wata 21 a kurkuku’

Kafofin yada labaran a kasar Spain sun ruwaito cewa an yankewa fitaccen dan kwallon kungiyar Barcelona Lionel Messi hukuncin daurin wata 21 a gidan yari. An kuma yankewa mahaifinsa ma Jorge Messi, hukuncin daurin sakamakon damfarar Spain Dala miliyan 4 da dubu 600 tsakanin shekarar 2007 da 2009. A yayin da ake gabatar da shari’ar, […]

‘Messi zai yi wata 21 a kurkuku’

Dan wasan Lionel MessiKafofin yada labaran a kasar Spain sun ruwaito cewa an yankewa fitaccen dan kwallon kungiyar Barcelona Lionel Messi hukuncin daurin wata 21 a gidan yari.

An kuma yankewa mahaifinsa ma Jorge Messi, hukuncin daurin sakamakon damfarar Spain Dala miliyan 4 da dubu 600 tsakanin shekarar 2007 da 2009.

A yayin da ake gabatar da shari’ar, masu shigar da kara sun ce ya yi amfani da kasashen Belize da Uruguay wajen boye kadarorinsa don gudun kada ya biya haraji.

Sai dai dan wasan kasar Ajentinan ya ce bai san komai kan lamarin.