Metuh ya yi yunkurin hadiye takardar bayaninsa ga EFCC

Kakakin Jam’iyyar PDP ta kasa Mista Olisa Metuh da Hukumar Yaki da yin wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ke rike da shi a babban ofishinta ya yayyaga takardar bayanin da ya yi wa hukumar a kashin kansa kuma ya yi yunkurin cinye ta.Wata majiya ta Hukumar EFCC ta shaida wa Aminiya cewa Metuh wanda ake […]

Metuh ya yi yunkurin hadiye takardar bayaninsa ga EFCC
Metuh ya yi yunkurin hadiye takardar bayaninsa ga EFCC

Kakakin Jam’iyyar PDP ta kasa Mista Olisa Metuh da Hukumar Yaki da yin wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ke rike da shi a babban ofishinta ya yayyaga takardar bayanin da ya yi wa hukumar a kashin kansa kuma ya yi yunkurin cinye ta.
Wata majiya ta Hukumar EFCC ta shaida wa Aminiya cewa Metuh wanda ake zarginsa da hannu a badakalar karkatar da kudin sayen makamai Dala biliyan 2 da miliyan 100 da ofishin toshon Mashawarcin Shugaban kasa, Kanar Sambo Dasuki (mai ritaya) da jagoranta, ya yayyaga bayanin ne lokacin da masu bincike suka gabatar masa domin ya sa hannu a kokarin da ake yi na gabatar da shi a gaban kotu.
Majiyar ta ce, ya yi yunkurin ya cinye takardar amma jami’an hukumar suka hana shi hadiye ta.
Majiyar ta ce, akwai yiwuwar Metuh ya damu da irin bayanan da ya ba hukumar don haka ne ya yi yunkurin lalata su.
Wata majiyar ta ce yanzu Hukumar EFCC tana duba yiwuwar sake tuhumar Metuh da karin laifuffuka biyu na lalata kayan gwamnati da gangan da kuma hana jami’an hukumar gudanar da ayyukansu.
Hukumar EFCC ta kama Metuh ne bayan da ta gano an tura masa Naira miliyan 400 a asusun wani kamfaninsa daga ofishin Dasuki.
A farkon wannan mako Shugaban Hukumar EFCC, Malam Ibrahim Mustafa Magu ya ce Mista Metuh ya ce zai gwammace ya shiga yajin cin abinci da ya mayar da kudin da ake zargin ya karkatar da su.
Daga baya-bayan nan kuma an ruwaito shi yana cewa zai bayyana irin aiki da ya yi da kudin da aka ba shi ne don yi wa Shugaba Goodluck Jonathan a gaban kotu ta yadda ba za a sauya abin da ya fada ba.
Wani mai tallafa masa, Richard Ihediwa, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Ya ce, Metuh ya karbi kudin ne daga tsohon Shugaban kasa don gudanar da aikin da aka ba shi, amma ana nema a jirkita gaskiyar lamari don a bata masa suna.